Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Jigon Siyasa a Jihar Kano

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Jigon Siyasa a Jihar Kano

  • Bashir Ahmad, Hadimin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari yace jam'iyya mai mulki ta ƙara karfi a mahaifarsa jihar Kano
  • A cewarsa, Sakataren jam'iyyar Labour Party (LP) ya sauya sheka zuwa APC, ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu
  • Wannan na zuwa ne yayin da APC ke fama da rikicin cikin gida wanda ya ja ta ɗage kaddamar da tawagar kamfe

Kano - Yayin da ake cigaba da shirin tunkarar babban zaɓen 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara karfi a jihar Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

Sakataren jam'iyyar Labour Party (LP) , Nasiru Umar D. Hajiya, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, ya tabbatar da goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu.

Tutar jam'iyyar APC.
Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Jigon Siyasa a Jihar Kano Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Babban mai taimaka wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na musamman kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad, shi ne ya bayyana haka shafinsa na Tuwita.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Machina Ya Kada Ahmad Lawan A Kotu, An Alantasa Matsayin Sahihin Dan Takara

A rubutun da ya saki a shafinsa, Bashir Ahmad yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sakataren jam'iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Kano ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC mai mulki."

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, daga kusu maso gbaashin Najeriya, shi ke neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP, sai dai wannan cigaban ba zai masa daɗi ba.

Jam'iyyar APC ta ɗage kaddamar da kamfe

A yau 28 ga watan Satumba, 2022, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta buɗe dama ga jam'iyyun siyasa su fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓenta. Wasu majiyoyi masu kwari sun nuna cewa an samu barkewar rikici kan waɗanda aka naɗa.

Wani rahoto ya nuna cewa da yawan gwamnonin APC sun nuna fushinsu kan wasu da aka naɗa da kuma rashin ganin sunayen mutanen su a kwamitin na mutum 422.

Kara karanta wannan

Jerin Rukunin Yan Kasuwa 6 da Liyafarsu Zata Ɗaga Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe Na 2023

A wani labarin kuma Jonathan, gwamnoni da wasu jiga-jigan PDP sun kauracewa taron kaddamar da tawagar Atiku

Taron kaddamar da wasu litattafai na Atiku Abubakar da tawagar Kamfe ya ƙara tabbatar da rikicin jam'iyyar PDP.

Tsohon shugaba, Goodluck Jonathan, gwamna Wike da sauran yan tawagarsa ba su halarci wurin taron ba a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262