Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

  • Jigon jam'iyyar PDP, Emeka Ihedioha, ya sanar da cewa daga Atiku ya kammala wa'adin mulkinsa, Kudu maso gabashin Najeriya ce zata karba ragama
  • Ya bayyana cewa, a halin yanzu da ake ciki a kasar nan, jam'iyyu biyu tak na PDP da APC kadai ake da su na siyasa
  • Ya tabbatar da cewa, shi din ne ke da sha'awa tare da burin jan ragamar kasar don shi ke akalar inda ya dace 'yan kabilar Ibo su bi

Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, ya ce shugabancin Najeriya zai koma yankin Kudu maso Gabas, bayan gwamnatin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ta kammala mulki, idan ya lashe zaben 2023.

Atiku da Ihedioha
Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Ihedioha ya sanar da hakan ne a wani bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

A cewarsa, jam’iyyu biyu ne kawai a zabukan 2023 masu zuwa, su ne PDP da All Progressives Congress, APC, jaridar Punch ta rahoto.

Ihedioha ya bayyana cewa 'yan Najeriya ba za su iya tafka kuskure a zaben 2023 ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Bari in fada muku, bayan Atiku Abubakar, shugaban Najeriya zai fito daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Dole ne ka yi nasara a Zamfara, Sokoto, Kebbi, Gombe, Borno, Yobe, Adamawa da sauransu sannan ka zama shugaban Najeriya.
“Dole ne ku yi shirin lashe zabe kuma a nan ne nake ciki. Ina so in gaya muku, ina da mabudin alkiblar inda ya kamata Igbo su bi.”

'Dan Hakin da Ka Raina: Kuri'un da Peter Obi Zai Samu Zasu Girgiza 'Yan Siyasa, Peter Ameh

A wani labari na daban, manyan 'yan siyasan fitattun jam'iyyu a kasar nan an ankarar da su kan cewa su yi taka-tsan-tsan kuma kada su zuba ido tare da raina 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, jaridar Independent ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

'Dan takarar majalisar dattawa na jam'iyyar LP a mazabar Ankpa, Peter Ameh ya sanar da hakan ga manema labarai a wani taro da aka shirya don masu takarar kujerun majalisa na jam'iyyar wanda aka yi a Lokoja dake jihar Kogi.

Ameh ya bayyana cewa, akasin yadda wasu 'yan siyasa suka sakankance na cewa 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ba shi da tsarin da ya dace yayi nasara a zaben, hakan ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng