Zaben 2023: Atiku Abubakar Zai Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP a Kudu Maso Gabas

Zaben 2023: Atiku Abubakar Zai Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP a Kudu Maso Gabas

  • Atiku Abubakar da gwamna Okowa na jihar Delta sun shirya taro da masu ruwa da tsakin PDP na shiyyar kudu maso gabas
  • Taron zai gudana a jihar Enugu gobe Talata 27 ga watan Satumba, 2022 matukar wani abu bai sa an canza ba
  • Kudu maso gabashin Najeriya na ganin an maida su saniyar ware a duk lokacin da ake batun takarar shugaban ƙasa a PDP

Abuja - Matukar ba'a samu wani canji a karshe ba, mai neman zama shugaban Najeriya a inuwar PDP, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, zasu gana da masu ruwa da tsaki na yankin kudu maso gabas.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa taron an shirya gudanar da shi a jihar Enugu, ɗaya daga cikin jihohin shiyyar kudu maso gabashin Najeriya, ranar Talata (Gobe) 27 ga watan Satumba, 2022.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

Gwamna Okowa tare da Atiku Abubakar.
Zaben 2023: Atiku Abubakar Zai Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP a Kudu Maso Gabas Hoto: Okowa, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Taron kamar yadda wasu bayanai suna tabbatar, zai gudana ne a wani ɓangaren yawon neman shawarin da mai neman zama shugaban ƙasan ke yi a matakin shiyya-shiyya.

Atiku ya gudanar da makamancin wannan taron da masu ruwa da tsaki na shiyyar kudu maso yamma a Ibadan, babban birnin jihar Oyo makon da ya gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me za'a tattauna a taron?

Legit.ng Hausa ta gano cewa ana tsammanin ƙusoshin PDP na shiyyar zasu gabatarwa Atiku jerin abubuwan da suke tsammani da muƙamai don cimma matsaya gabanin babban zaɓen 2023.

Kudu maso gabashin Najeriya sun koka kan yadda ake jingine su a duk lokacin da ake batun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Jagororin jam'iyyar sun yi iƙirarin cewa shiyyar ta cancanci abinda ya zarce haka idan aka yi la'akari da yadda suka rike PDP hannu bibbiyu tun farkon kafata a 1998.

Kara karanta wannan

Siyasar 2023: Atiku Abubakar Ya Canza Salo, Ya Fara Kulle-Kullen Wargaza Karfin Gwamna Wike

Atiku ya tabbatar da shirya zaman

Sa'ilin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Mr. Charles Aniagu, yace, "Eh tabbas, an shirya taro a jihar Enugu gobe (Talata)"

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu

Fadar shugaban kasa ta magantu a kan rade-radin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi a cire Festus Keyamo a kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana ikirarin a matsayin karya mara tushe balle makama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262