Shugaban Kasa A 2023: Peter Obi Na Kara Yin Suna Da Karfi, Babban Jigon APC Ya Yi Hasashe Mai Karfi
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya yi hasashen cewa jam’iyyar Labour Party za ta dare PDP a zaben 2023
- Fani-Kayode wanda ya kasance jigon APC ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi na kara karfi gabannin zaben
- Sai dai kuma ya ce duk da wannan shahara na Obi, ba zai taba dare jam’iyyar APC mai mulki da dan takararta, Bola Tinubu ba
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya magantu a kan karfin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ke samu gabannin babban zaben 2023.
Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook, yana mai bayyana bunkasar da Peter Obi ya samu a tseren shugabancin kasar a matsayin wani lamari da ke tattare da lauje a cikin nadi.
Ya tabbatar da cewar sunan Obi na tashi cikin sauri kuma yana kara samun karfi yayin da yayi hasashen cewa jam’iyyar LP za ta dare PDP a matsayin babbar jam’iyyar adawar kasar a zaben 2023 mai zuwa.
Sai dai kuma ya jaddada cewa koda za a hada LP da PDP ba za su iya ja da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya rubuta a shafin nasa:
“Obi na tashi cikin sauri kuma yana kara karfi. Akwai lauje cikin nadi a tashin nasa.
“A wannan halin shi da magoya bayansa za su iya dare PDP wajen zama babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.
“Sai dai idan aka hada su dukka biyun ba za su iya karawa da magoya bayan Jagaban na babbar jam’iyyar APC ba!”
Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023
A wani labarin kuma, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David, ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, da kokarin raba kawunan coci.
Babachir ya bayya cewa a kokarinsa na ganin ya shawo kan masu zabe sun yarda da tikitin addini guda, Tinubu ya tanadi kungiyoyin kirista na bogi don raba kan coci, jaridar The Sun ta rahoto.
Jigon na APC ya ce wasu yan Najeriya sun tuntube shi da tsohon kakakin majalisar, Yakubu Dogara, don shawo kansu su yarda da tikitin Musulmi da musulmi na APC.
Asali: Legit.ng