2023: Atiku Ya Fara Shirye-Shiryen Wargaza Karfin Wike, Zai Jawo Yaransa

2023: Atiku Ya Fara Shirye-Shiryen Wargaza Karfin Wike, Zai Jawo Yaransa

  • Mai neman kujerar shugaba Buhari a 2023 karkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya fara wani shirin haɗa kan jam'iyya
  • Yayin da gwamna Wike ya banɗare aka gaza gano manufarsa, Atiku ya fara kulla yadda zai jawo yaransa su canza ra'ayi
  • Tsagin gwamnan Wike na kokarin maye gurbin Iyorchia Ayu da tsohon gwamnan jihar Ondo

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gama wasu shirye-shiryen wargaza ƙarfin da gwamna Nyesom Wike na Ribas ke taƙama da shi.

Wasu alamu masu karfi na nuna cewa Wike da masu goyon bayansa sun kokarin cusa tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, a matsayin wanda zai maye gurbin shugaban PDP na ƙasa idan buƙatarsu ta biya.

Atiku Abubakar.
2023: Atiku Ya Fara Shirye-Shiryen Wargaza Karfin Wike, Zai Jawo Yaransa Hoto: vangaurdngr.com
Asali: Twitter

Atiku da Wike na takun saƙa kan sauya Ayu

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa gwamna Wike ya sha alwashin gyara zama a jam'iyyar PDP ba zai sauya sheƙa ba kan rikicinsa da Atiku, inda ya jaddada cewa zai zauna ya cigaba da yaƙi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma idan dai baku manta ba wasu daga cikin makusantan Wike sun sanar da matakin janye wa daga tawagar yaƙin neman zaben ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, gwamna Okezie Ikpeazu na Abiya da Seyi Makinde na Oyo sun tsame kansu har zuwa lokacin da Ayu zai yi Murabus.

Sauran mambobin tsagin Wike sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban PDP, Olabode George Donald Duke, Ayo Fayose, Ibrahim Dakwanmbo, Segun Mimiko, Jonah Jangda sauran su.

Atiku ya soma kulle-kullen karya ƙarfin Wike

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan PDP, Gwamna Wike Ya Yi Sabuwar Tafiya

Wasu majiyoyi mabanbanta sun gaya wa Vanguard cewa Atiku da wasu jagororin PDP sun fara tuntuɓar wasu daga cikin yaran Wike da nufin jawo hankalinsu su maida wukarsu kube kana su yi aiki domin nasarar PDP a 2023.

Wata majiya da ta yi bayani da sharaɗin boye bayananta tace:

"Akwai wani hange da ake a jam'iyya kan cewa ba abinda gwamna Wike zai rasa amma na kusa da shi ka iya yuwuwa a kaisu a baro yayin da wasun su basu da madafa."
"Waɗanda suke da abin dogaro za'a iya girbe su kuma wannan abu ne mai kyau sabida waɗan nan mutane ba su ƙaunar juya wa Wike baya, sun san zai iya magana a kansu."

Wata majiyar ta daban tace tsohon mataimakin shugaban kasan ya ɗauri ɗamarar rarrashin mambobi da shugabannin PDP da suka fusata.

"Akwai wasu matakai a cikin gida da aka fara bi da nufin jawo ra'ayin waɗannan mutanen (Na kusa da Wike) a haɗa kai da su don tabbatar da nasarar jam'iyya a 2023."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

"Bisa adalci waɗannan mutanen ba zasu iya yaƙar Wike ba, mu bamu san manufarsa ba haka su kansu dake ikirarin suna tare da shi basu san ainihin inda ya sa gaba ba."

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan Na Gab Sanin Makomar takararsa a 2023

Babbar Kotun tarayya dake Damaturu ta shirya gabatar da hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a mazaɓar Sanatan Yobe ta arewa.

Bashir Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwani a watan Mayu ne ya kai ƙarar domin neman hakkinsa da ake neman danne masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262