Ka Da Ku Yi Kuskuren Zaben Shugabanni Masu Kisa a 2023, Jonathan Ga Yan Najeriya

Ka Da Ku Yi Kuskuren Zaben Shugabanni Masu Kisa a 2023, Jonathan Ga Yan Najeriya

  • Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya gargaɗi 'yan Najeriya su yi takatsantsan wajen zaɓen shugabanni a 2023
  • Jonathan yace duk ɗan takarar da ya ɗauki makami ya yi kisa don zama shugaba, haka zai ci gaba da aikata wa
  • Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, bisa dumbin ayyukan ci gaba da ya yi wa talakawansa

Akwa Ibom - Yayin da ake tunkarar babban zaɓe, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya gargaɗi 'yan Najeriya kar su yi kuskuren zaɓen wasu shugabanni da ya kira "Masu kisa" a zaɓen 2023.

Jonathan ya yi wannan gargaɗin ne ranar Lahadi a Uyo a wurin wani taron Addu'o'in godiya na musamman na bikin cikar jihar Akwa Ibom shekara 35 da kafu wa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Ka Da Ku Yi Kuskuren Zaben Shugabanni Masu Kisa a 2023, Jonathan Ga Yan Najeriya Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook
"A zaɓen 2023, ya zama tilas ku kula kada ku yi kuskuren zaɓen shugabanni masu aikata kisa, waɗanda ke ɗaukar wuƙaƙe, bindigu, da sauran makamai su kashe mutane saboda siyasa."
"Idan ka kashe mutane don kawai ka zama shugaba, haka zaka ci gaba da kashe mutane don ka zauna a kujerarka. Mutane zasu ci gaba da shan wahala ne kawai."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ku tabbata tun daga majalisar dokokin jiha zuwa majalisar wakilan tarayya da Sanatoci da gwamna kun zabi mutane masu amana da aka yarda da su a jihar Akwa Ibom."

- Goodluck Jonathan.

Jonathan ya yaba wa gwamnan Akwa Ibom

Tsohon shugaban ƙasan ya yaba wa gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom bisa yadda ya ba mara ɗa kunya wajen ayyukan cigaba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Ya haƙaito lokacin da tsohon gwamna, Godswill Akpabio, ya bar Ofis, an yi hangen rashin tabbas game da kokarin gwamna Emmanuel, wanda a lokacin yana Sakataren gwamnati.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar PDP Ta Zaɓi Ranar Sake Sabon Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Arewa

Duk da Udom Emmanuel ya shiga siyasa ne daga ɓangaren masu cin gashin kansu, Jonathan yace gwamnan ya yi abinda ya dace a shekara Bakwai da hawa madafun iko, Premium Times ta ruwaito.

A wani labarin kuma Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Tun farko dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya nuna cewa dalilinsa na zabar musulmi a matsayin abokin takara ba saboda addini bane.

Babachir David Lawal ya zargi Tinubu da kulla-kulla da son raba kan mabiya addinin kirista a kokarinsa na shawo kan mutane su yarda da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262