Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

  • Tun farko dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya nuna cewa dalilinsa na zabar musulmi a matsayin abokin takara ba saboda addini bane
  • Babachir David Lawal ya zargi Tinubu da kulla-kulla da son raba kan mabiya addinin kirista a kokarinsa na shawo kan mutane su yarda da shi
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya jadadda cewa ya zabi Kashim Shettima ne saboda yana nufin yan Najeriya da alkhairi

Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David, ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, da kokarin raba kawunan coci.

Babachir ya bayya cewa a kokarinsa na ganin ya shawo kan masu zabe sun yarda da tikitin addini guda, Tinubu ya tanadi kungiyoyin kirista na bogi don raba kan coci, jaridar The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Shettima da Tinubu
Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023 Hoto: @officialBAT
Asali: Twitter

Jigon na APC ya ce wasu yan Najeriya sun tuntube shi da tsohon kakakin majalisar, Yakubu Dogara, don shawo kansu su yarda da tikitin Musulmi da musulmi na APC .

Daga Babachir har Dogara sun nuna adawarsu da wannan tsari da jam'iyyar mai mulki ta bi inda suke ci gaba da tattaunawa da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannunsa wanda aka gabatarwa da manema labarai ta hannun tawagar yada muradunsa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Wani bangare na Babachir na cewa:

"Zuwa yanzu dai bamu dauki hanyar sulhu ba saboda a matakin farko, daga APC a matsayinta na jam'iyya har dan takararta da shugaban kasa basu damu da neman yin sulhu da mu ba duk da cewar mun bayar da kafar yin haka.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Wa Wike Tayin Kujerar Sanata? Gwamnan Na Rivers Ya Fayyace Gaskiya

"Kawai dai mun ji ra'ayoyinsu ne ta farfaganda da ake yadawa a kafofin watsa labarai bisa la'akari da yawan sukar da suke sha.
"Shakka babu akwa wasu kiristoci da Yahudawa wadanda saboda dakushewar dabi'a, talauci ko hadama suka bayar da hayar kansu a matsayin wakilai da masu bata addinin kiristanci."

Allah Bai Gaya Mun Magajin Buhari Ba, Malamin Addini Ya Magantu Kan Zaben 2023

A wani labarin, baabban limamin cocin Deeper Christian Life Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah bai yi masa wahayi game da wanda zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba ba.

Sai dai kuma ya yi alkawarin bayyanawa duniya da zaran Allah ya sanar da shi wanene shugaban kasar Najeriya na gaba, jaridar The Nation ta rahoto.

Kumuyi ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, jihar Neja yayin wani taro da ya gudana a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng