Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Wasu 'Ya'Yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC Ana Tsaka da Rikici

Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Wasu 'Ya'Yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC Ana Tsaka da Rikici

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi babban kamu a jihar Oyo gabannin babban zaben 2023
  • Mabobin manyan jam'iyyun adawa ta PDP da SDP da dama sun sauya sheka zuwa jam'iyyar mai mulki a kasar
  • Sun sha alwashin yin aiki domin ganin dan takarar gwamna na jam'iyyar a jihar, Sanata Teslim Folarin ya lashe zabe

Oyo - Wasu mambobin jam’iyyar siyasa a jihar Oyo sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin babban zaben 2023.

Masu sauya shekar sun samu tarba a ranar Asabar yayin wani taron jam’iyyar da ya gudana a makarantar sakandare na Elekuro, Ogbere a yankin Ona-Ara da ke jihar.

Wadanda suka jagoranci taron na maraba da zuwa sune, Sanata Teslim Folarin, dan takarar gwamna na APC a jihar da Dr Yunus Akintunde, dan takarar sanata mai wakiltan Oyo ta tsakiya, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Kara Shiga Tsaka Mai Wuya, Wasu 'Ya'yan PDP a Arewa Sun Koma Tsagin Wike

Mambobin APC
Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Wasu 'Ya'Yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC Ana Tsaka da Rikici Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A madadin Folarin, shugaban hukumar caca ta kasa, Alhaji Fatai Ibikunle, ya yiwa masu sauya shekar maraba da zuwa APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ibikunle ya basu tabbacin samun adalci da daidaito a sabuwar jam’iyyarsu, yana mai alkawarin cewa za su amfana daga kowace dama game da jin dadin ‘ya’yan jam’iyya ba tare da wariya ba.

Ya ce:

“Ina maku maraba da zuwa jam’iyyarmu, APC, a matsayin sabbin mambobi kuma ina bakun taccin samun dukkanin yancin da sauran mambobinsu zasu samu.
“Za mu tabbatar da ganin cewa kun amfana daga kowace irin dama game da jin dadin ‘ya’yan jam’iyya ba tare da son kai ba.”

Ya bukaci sabbin mambobin da su tattaro jama’a don nasarar yan takaran APC a zaben 2023, rahoton Vanguard.

Mogaji Akinjide, wanda ya jagorancin masu sauya sheka daga PDP, ya ce sun ji dadin kwarya-kwaryar da Folarin ya shirya masu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike

Yayinda Elder A Kalejaye, wanda ya jagoranci masu sauya sheka daga SDP, ya ce kokarin Folarin da zamowarsa dan takarar gwamna na APC ne yasa suka sauya sheka.

A cewarsa, nasarar APC a zaben 2023 zai amfani karamar hukumar Ona-Ara dama jihar baki daya.

Folarin ya jinjinawa masu sauya shekar, yana mai cewa sun yanke hukunci mai kyau ta hanyar dawowa APC.

A halin yanzu, ya yi alkawarin tafiya tare da masu sauya shekar a dukkan harkokin jam’iyyar da kuma tabbatar da ganin cewa sun amfana daga damammakin.

Dan takarar gwamnan ya bukace su da su tafi ungunninsu mabanbanta zannan su dunga halartan tarukan jam’iyyar akai-akai don samun karin bayani game da jam’iyyar.

Allah Bai Gaya Mun Magajin Buhari Ba, Malamin Addini Ya Magantu Kan Zaben 2023

A wani labarin, babban limamin cocin Deeper Christian Life Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah bai yi masa wahayi game da wanda zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba ba.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Jam’iyyar Atiku Ta Juya Masa Baya, Za Tayi Wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Sai dai kuma ya yi alkawarin bayyanawa duniya da zaran Allah ya sanar da shi wanene shugaban kasar Najeriya na gaba, jaridar The Nation ta rahoto.

Kumuyi ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, jihar Neja yayin wani taro da ya gudana a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng