Janar Buratai, Tsofaffin Jami’an Tsaro 10 da ke Cikin Kwamitin Yakin Zaben Bola Tinubu
Abuja - A ranar Asabar aka ji labari an fitar da sunayen wadanda za su yi wa Asiwaju Bola Tinubu aikin yakin neman takarar shugaban kasa a APC.
Legi.ng ta bibiyi cikakken jerin da jam’iyyar APC ta fitar na kwamitin mutum 422, ta fahimci akwai tsofaffin jami’an tsaro da za su bada gudumuwarsu.
Ga jami’an sojoji da suka yi ritaya da sunayensu ya shiga cikin kwamitin yakin neman zaben:
1. Air Marshall Siddique Abubakar
Tsohon shugaban hafsun sojojin sama, Air Marshall Siddique Abubakar mai ritaya shi ne Shugaban yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihar Bauchi.
2. Janar Tukur Yusuf Buratai
Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya samu matsayin Mataimakin Darekta a kwamitin tsaro. Buratai wanda yanzu Jakada ne ya yi shugaban sojojin kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Janar Abdulrahman Bello Dambazzau
Wani tsohon hafsun sojojin kasa a jerin shi Janar Abdulrahman Bello Dambazzau mai ritaya. Tsohon Ministan yana cikin masu bada shawara wajen dabaru.
4. Janar Mohammed Magoro
Janar Mohammed Magoro (mai ritaya) yana cikin iyayen kwamitin takaran na 2023. Magoro ya rike mukaman Minista da Sanata a Kebbi da ya yi ritaya a soja.
5. Janar Jibril Abdulmalik
Darektan kwamitin tsaro na kwamitin yakin neman zaben shi ne Manjo Janar Jibril Abdulmalik mai ritaya, zai jagoranci wasu tsofaffin sojoji a wannan kwamitin.
6. Janar Abayomi Olanishakan
Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya) zai taimakawa tsohon shugaban PTTDS wajen wannan aiki. Shi ma Olanishakan ya rike gidan soja daga shekarar zuwa 2021.
7. Janar Ladan Yusuf
Birgediya Janar Ladan Yusuf ya samu shiga cikin wannan kwamiti a matsayin Magatakarda. Yusuf ya taba zama mai ba gwamnan Bauchi shawara a harkar tsaro.
8. Janar Patrick Akpa
Sunan Manjo Janar Ademu Akpa (Rtd) ya fito a kwamitin. Tsohon sojan ya dade da zama ‘dan siyasa, domin ya yi takarar gwamna a jihar Kogi a karkashin APC.
Sauran jami’an tsaro
A jerin akwai wasu tsofaffin jami’an tsaron baya ga sojoji. Mun fahimci kwamitin yana kunshe da tsohon jami’in hukumar kwastam da tsohon Sufetan ‘yan sanda.
9. IGP Musliu Smith (mai ritaya)
10. DCG Garba Goronyo
Babu sunan Osinbajo
Kun ji labari an ki daukar Yemi Osinbajo, tsohon sakataren gwamnati da tsohon shugaban majalisa da wasu kusoshin APC a kwamitin yakin zaben na badi.
A 'yan kwamitin mai mutum fiye da 400, mun ji akwai sauran wadanda suka yi takara da Bola Tinubu a APC irinsu Rotimi Amaechi da Dr. Ahmad Lawan.
Asali: Legit.ng