Ganduje Ya Bayyana Abin Da Mulkin Tinubu Za Ta Kawo Wa Najeriya

Ganduje Ya Bayyana Abin Da Mulkin Tinubu Za Ta Kawo Wa Najeriya

  • Abdullahi Ganduje, gwamnan Jihar Kano ya ce Najeriya za ta samu cigaba da alheri cikin kankanin lokaci idan aka zabi Tinubu a 2023
  • Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a gidan gwamnatin jihar Kano
  • Ganduje ya bayyana Tinubu a matsayin kwararre kuma daya cikin wadanda suka yi gwagwarmaya don kafa demokradiyyar a ake mora a Najeriya

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da wasu manyan yan Najeriya sun ce gwamnatin Tinubu a 2023 zai gaggauta cigaba da bunkasa a kasar, rahoton The Nation.

Ganduje ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amincewa da nadin da aka masa matsayin majibinci na kungiyar APC na hadin kan kasa (ANIM) a gidan gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Ana Samun Rabuwar Kai a Kamfe Saboda Tinubu Ya Jawo Gwamna, Ya Ba Shi Mukami

Tinubu d Ganduje.
Ganduje Ya Bayyana Abin Da Mulkin Tinubu Za Ta Kawo Wa Najeriya. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce:

"Ayyukan da Asiwaju Tinubu ya yi a baya sun nuna cewa zai iya habaka Najeriya zuwa mataki na gaba, idan an zabe shi shugaban kasa.
"Asiwaju mutum ne mai gaskiya kuma haja ne mai kyau. Ya bada gudunmawa sosai wurin habaka da cigaban demokradiyyar mu.
"Asiwaju ƙwararren ɗan siyasa ne kuma jagoran masu son kawo cigaba da suka kawo demokradiyya da muke mora a Najeriya yanzu."

Jawabin shugaban ANIM

Jagoran ANIM na kasa Sadik Fakai ya ce an nada gwamnan na Kano ne don nuna godiya bisa rawar da ya taka don ganin Asiwaju Bola Tinubu ya zama ɗan takarar shugaban kasar na APC.

Kuma, tsohon kwamishinan Lafiya na jihar Legas, Dr Jide Idris, a jiya ya ce yan Najeriya su zabi Asiwaju Tinubu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC Ya Bayyana Adadin Kuri'un Da Tinubu Zai Samu Daga Yankin Yarbawa

Ya bawa yan Najeriya cewa tsohon gwamnan na Jihar Legas zai maimaita ayyukan alherin da ya yi a Legas ga kasa baki daya.

Ba Buhari Bane Matsalar Najeriya, Ku Dena Dora Masa Laifi, In Ji Babban Malamin Addini

A wani rahoton, malamin addini dan Najeriya mazaunin Birtaniya kuma babban fasto a cocin Faith Tabernacle, Apostle Alfred Williams, ya ce kada a dora wa Buhari laifi bisa matsalolin Najeriya.

Williams ya ce tsarin yadda Najeriya ta ke ne ke kawo cikas ga kyawawan niyya da Buhari ke da shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164