Gwamnonin PDP Sun Bayyana Shirin Da Suka Don Magance Rikicin Atiku da Wike

Gwamnonin PDP Sun Bayyana Shirin Da Suka Don Magance Rikicin Atiku da Wike

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun ce suna cigaba da tattauna wa tsakaninsu da nufin magance rikicin jam'iyya
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal, yace nan ba da jimawa ba duk wannan rikicin zai zama tarihi a PDP
  • Shugaban BoT na ƙasa, Sanata Adolphus Wabara, yace burin jam'iyyar PDP ta wayi gari a fadar shugaban ƙasa

Abuja - Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya tabbatar wa mambobi da jagororin jam'iyya cewa nan gaba kaɗan zasu magance rikicin da ya hana jam'iyyar motsi.

Tambuwal ya ba da wannan tabbacin ne bayan gana wa da mambobin kwamitin amintattu BoT bisa jagorancin Sanata Wabara a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Atiku Abubakar da Gwamna Wike.
Gwamnonin PDP Sun Bayyana Shirin Da Suka Don Magance Rikicin Atiku da Wike Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya shaida wa mambobin BoT cewa shi da sauran takwarorinsa tuni suka fara laluben hanyar warware dukkanin saɓanin da suka yi wa jam'iyyar katutu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal ya karbe mukamin shugaban gwamnonin Najeriya

A kalamansa, gwamna Tambuwal yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina mai gode wa shugaban BoT, mambobi da 'yan tawagarsa bisa wannan tafiya da suka fara mai matuƙar amfani. Kowa ya san cewa BoT wani ginshiki ne a jam'iyya, a duk lokacin da aka samu matsala irin wannan, su ke tsoma baki."
"Mun tattauna da su kuma ina tsammanin suna gab da lalubo maganin matsalar da ta addabe mu. Ina ƙara baku tabbacin gwamnonin jam'iyya mun fara tattauna wa tsakanin mu nan ba da jima wa ba zamu zauna."
"Dukan mu muna sha'awar zama inuwa ɗaya da aiki tare kan wata manufa kuma wannan manufa ta jam'iyya ce da yan Najeriya saboda kowa ya gaji da gwamnatin APC. Muna kokarin sallamar APC nan da watan Mayu."

Burin mu shiga Aso Villa - BoT

Tun da farko, shugaban BoT na ƙasa, Sanata Wabara, ya jaddada kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba 'yan Najeriya zasu sha mamaki a PDP.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Wike Ya Matsa Lamba, Ya Kira Taron Jiga-Jigai da Masu Ruwa da Tsakin PDP

A ruwayar Daily Trust, Wabara yace:

"Burin mu shi ne mu wayi gari a Aso Villa, idan har muna son ganin PDP ta shiga Aso Villa to akwai bukatar kowa ya ba da haɗin kai. Muna cigaba da zagaye nan da kwana 6 za'a fara Kamfe, muna son kafin lokacin PDP ta dunƙule."

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Sanya Ranar Canza Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamnan Zamfara

Jam'iyyar PDP tace zata gudanar da sabon zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan Zamfara a 2023 bayan Kotu ta soke na baya.

Shugaban PDP a jihar, Sani Ƙaura, yace shirye shirye sun yi nisa domin bin umarnin Kotu gobe Jumu'a 23 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262