2023: Gwamnan PDP Ya Bayyana Matsayin Jam'iyyar Kan Janyewar Wike Da Mutanensa Daga Takarar Atiku
- Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin da ke faruwa a jam'iyyar ta PDP
- Gwamnan wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya bukaci yan Najeriya musamman yan siyasa su rika cika alkawari da suka dauka
- Jigon na PDP ya yi wannan kiran ne, awanni bayan mutanen Wike sun fita daga kwamitin yakin neman zaben Atiku
Shugaban kungiyar yakin neman zaben takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Udom Emmanuel, ya jadada bukatar da ke akwai na mutane su rika cika alkawarin su.
Gwamnan na Jihar Akwa Ibom ya yi wannan kiran ne yayin da ya ke martani kan janyewar mutanen Gwamna Nyesom Wike daga kwamitin kamfen din na PDP, Rivers Mirror ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya dage dole sai Ayu ya sauka daga mukaminsa
Bangaren Wike na bukatar shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus kuma a bawa kudu kujerar shugabancin jam'iyyar.
An, rahoto cewa Ayu ya yi alkawarin cewa zai iya murabus idan dan arewa ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP.
Amma, akwai alamun ya ki cika 'alkawarin' ya dage sai ya cika wa'adinsa na shekara hudu.
Gwamna Udom ya yi martani
Da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na Channels TV, ranar 22 ga watan Satumba, gwamnan ya ce ya kamata yan Najeriya su koya cika alkawarin da suka dauka.
Ya ce:
"Abu daya da na gano a siyasa da rayuwa shine mutane su rika kokarin su yi abin da suka ce za su yi. Wannan shine sababin matsalolin.
"Da zarar mun fara cika alkawarin mu a matsayin kasa, hakan zai zama alheri a gare mu."
Gwamna Udom ya yi magana kan sauke Ayu
Da ya ke martani kan cewa dole a bi doka wurin sauke Ayu, gwamnan ya ce ko da abu ba kan doka ya ke ba, ana iya yi don zaman lafiya.
Ya kuma bayyana cewa yana fatan za a warware matsalin jam'iyyar.
Rikicin PDP: Ba'a Yi Wa Gwamna Wike Adalci Ba Kwata-Kwata, Ortom
A wani rahoton, Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce jam'iyyar PDP ba ta kyauta wa takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, ba.
Gwamna Ortom ya yi wannan furucin ne a wurin taron 'ya'yan PDP da ya gudana ranar Litinin a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng