Babu Tabbacin Ahmad Lawan Zai Dawo Majalisa, Zai Rasa Takarar Farko Tun 1999

Babu Tabbacin Ahmad Lawan Zai Dawo Majalisa, Zai Rasa Takarar Farko Tun 1999

  • Ahmad Ibrahim Lawan yana cikin wadanda aka ga babu sunansu a cikin wadanda za su yi takara
  • Rikicin da ake yi tsakanin Sanata Ahmad Lawan da Bashir Machina ya sa APC ba ta da ‘Dan takara a 2023
  • Jam’iyyar APC za ta iya asarar kujerar Sanata na shiyyar Arewacin jihar Yobe idan har aka tafi a haka

Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan bai cikin sunayen ‘Yan takaran da hukumar zabe na INEC ta fitar a makon nan.

A ranar Talatar nan Hukumar zabe ta wallafa sunayen wadanda za su shiga takarar shugaban kasa, majalisar dattawa da majalisar wakilai a zabe mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta bi sunayen ‘yan takaran da za a gwabza da su, ta fahimci idan aka tafi a haka, Ahmad Ibrahim Lawan ba zai yi takarar komawa majalisa ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: INEC bata manna sunan Shekarau a matsayin dan takarar sanata a PDP ba

Rikicin shugaban majalisar da Hon. Bashir Machina ya yi sanadiyyar da jam’iyyar APC ta rasa ‘dan takarar kujerar majalisar dattawa a yankin Yobe ta Arewa.

A gefe guda kuma, mun ga cewa Sanata Ibrahim Gaidam da Bomai Ibrahim Mohammed za suyi wa APC takarar Sanatoci a Gabas da Kudancin Yobe.

Tun 1999 Lawan ya je Majalisa

Tun 1999, Ahmad Lawan ya zama ‘dan majalisar wakilai na shiyyar Bade da Jakusko. A 2003 ya zama Sanata da Usman Albashir ya nemi takara Gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan Hoto: @TheSenatePresident / Tope Brown
Asali: UGC

Idan har Lawan bai samu tikitin majalisar dattawa a zabe mai zuwa ba, wannan zai zama karon farko tun shekarar 1999 da bai tsaya takara a jihar Yobe ba.

PDP, NNPP da ADC sun tsaida ‘yan takara

Yayin da APC mai mulki take rigima a kan takarar, sauran jam’iyyu suna da ‘yan takararsu. NNPP da PDP sun tsaida Dayyabu Garba Hamza da Bello Ilu.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Sai da Buhari Ya Kira Janar Buba Marwa ta Wayar Salula

Sheriff Alhaji Bunu ne ‘dan takaran jam’iyyar ADC na kujerar Sanatan Arewacin Yobe a 2023.

'Yan takara 4000 sun samu shiga

Premium Times tace a zaben na 2023, ‘yan takara 1, 101 suka fito a karkashin jam’iyyu 18, suna neman kujerun majalisar dattawa 109 da ke kasar nan.

A gurbin majalisar wakilan tarayya, ‘yan takara 3, 122 za su gwabza a kan kujeru 360 a 2023. Legit.ng Hausa ta gano Yobe tana da 'yan takara 36 a nan.

Wannan ne karo na biyu da INEC ta ki sa sunan Ahmad Lawan a ‘yan takara. Haka aka yi a watan Yuni da aka fara fito da sunayen masu neman mulki.

Machina ya soki Shugaban APC

A baya, an samu rahoto Bashir Sheriff Machina ya maida martani bayan hirar da aka yi da Sanata Abdullahi Adamu a kan kujerar da suke fada a kai.

Hon. Machina ya karyata shugaban APC na kasa, ya ce sam Ahmad Lawan bai nemi takara a jihar Yobe ba, amma jam'iyya ta mikawa INEC sunansa.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng