Jam'iyyar PDP Ta Bullo da Sabon Salo, Malaman Musulunci Sun Gudanar da Addu'a a Cikin Ruwa Kan Zaben 2023

Jam'iyyar PDP Ta Bullo da Sabon Salo, Malaman Musulunci Sun Gudanar da Addu'a a Cikin Ruwa Kan Zaben 2023

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta koma ga Allah a yayin da ake shirin fara kamfen da gabatowar zaben 2023
  • An gano malaman Musulunci da fastoci suna rokon Allah alfarma yayin da ruwan sama ke bugunsu
  • Musamman aka shirya taron don neman nasarar jam'iyyar a babban zabe mai zuwa tare da addu'an neman rabuwan kan jam'iyya mai mulki

Ogun - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun ta mika lamuranta ga Allah inda ta tashi tsaye da addu’o’i kan babban zaben 20023.

A wasu hotuna da suka yadu a intanet, an gano wasu malaman addini durkushe a cikin ruwan sama kamar da bakin kwarya suna masu addu’o’i a garin Abeokuta, babban birnin jihar.

Taron addu’an ya gudana ne a sakatariyar PDP, wanda ke kusa da ofishin Gwamna Dapo Abiodun, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Hadimin Gwamnan Kaduna da Mambobin APC Sama da 13,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Malamai
Jam'iyyar PDP Ta Bullo da Sabon Salo, Malaman Musulunci Sun Gudanar da Addu'a a Cikin Ruwa Kan Zaben 2023 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A wajen taron, mambobin jam’iyya da malaman addinin da suka yi biris da ruwan sama sun yi addu’a cikin kankan da kai don neman goyon bayan Ubangiji yayin da kamfen da zabe ke kara gabatowa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama’ar wadanda suka gudanar da addu’o’insu musamman don nasarar jam’iyyar a zaben, sun kuma yi addu’o’in neman raba kan jam’iyya mai mulki, musamman a jihar.

Da yake magana a taron, sakataren jam’iyyar, Sunday Solarin ya ce:

“Koda dai mutane basa yin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya zama dole jam’iyyar ta nemi kariya daga masu bita da kulli da za su so tarwatsa shirin da PDP ta rigada tayi.”

Ya kara da cewa shugabannin matan jam’iyyar ne suka bayar da shawarar yin taron addu’o’in, yana mai cewa ya kasance irinsa na farko da jam’iyyar tayi a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

Da take jawabi ga manema labarai a gefen taron, shugabar mata ta jihar, Remilekun Olusoji, ta ce addu’an ya zama dole don kare kai daga miyagu a lokaci da bayan kafen.

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya nuna karfin gwiwa cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Sanata Bola Ahmed Tinubu, zai iya dawo da Najeriya kan tafarkin ci gaba idan ya dare kujerar shugabanci.

Gwamna Bello, wanda ya ce kungiyar yakin neman zaben BAT ta nada shi a matsayin jagoran matasa na kasa, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin ganawa da yan takarar kujerun ciyamomi da sauran masu ruwa da tsaki daga mazabar Idah ta jihar.

Ya bayyana cewa Tinubu yana bin tsarin jam’iyyar a kullun, ya nuna alkibla da shugabanci irin wanda kasar ke bukata don magance matsalolinta don haka dole a bashi goyon baya tare da zabarsa a 2023.

Kara karanta wannan

ObiDatti23: Lauyoyi 9 Sun yi Gayya, Sun Shigar da Karar Peter Obi da LP a Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng