Gwamna Buni Ya Karɓi Daruruwan Masu Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC a Yobe
- Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karɓi ɗaruruwan masu sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC
- Daga cikinsu har da ɗan takarar da ya nemi tikitin gwamna a PDP, Abba Gana Tata, Buni ya nuna jin daɗinsa da sauya sheƙar jigon
- Yace Abba Tata ba karamar kadara bane a siyasa, da shi aka kafa PDP, karo na farko da ya fice jam'iyyar tun 1998
Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya karɓi ɗaruruwan masu sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP bisa jagorancin, Alhaji Abba Gana Tata, ɗan takarar mataimaki a 2011 yayin da suka shiga APC.
Da yake jawabi a wurin taron tarbansu da aka shirya a Damaturu, Gwamna Buni yace Tata ba ƙaramin kadara bace mai girma a siyasa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan ya nuna tsantar farin ciki da sauya shekar Tata, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP, wanda ya fice daga jam'iyyar a karon farko tun shekarar 1998.
Mala Buni ya roƙi sauran mambobin dake tsagin hammayya su sake nazari kana su koma APC, inda a cewarsa jam'iyyar na da isasshen wuri da zai ɗauki baki ɗaya yan siyasan Yobe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tsohon shugaban APC na riko, Buni, yace ya yi wannan rokon ne saboda burinsa na haɗa kan al'ummar Yobe da kuma magance rikici da ta'adi tsakanin yan siyasa.
Meyasa suka zaɓi koma wa APC?
Tun farko, mai taimaka wa gwamna kan harkokin siyasa da majalisa, Alhaji Aji Bularafa, yace kyawawan ayyukan mai girma gwamna ne suka kwaɗaitar da Tata ya shiga APC.
A nasa jawabin, Abba Gana Tata, wanda ya nemi tikitin takarar gwamna a zaɓen 2023 karkashin PDP, yace kyakkyawan tsarin gwamna Buni da haba-habo da mutane ya ƙara masa kwarin guiwar shiga APC.
2023: Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na'Abba, Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Ya Fallasa Sirrin APC
Ya gode wa sabuwar jam'iyyarsa bisa kyakkyawan tarba hannu bibbiyu da aka musu kuma ya sha alwashin kasancewa mai biyayya da haɗin kai ga shugabanni.
A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku Ya Kafa Sharuddan Tunbuke Shugaban PDP Na Kasa Gabanin Zaben 2023
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace sauke Ayu abu ne mai sauki amma dole a bi matakan doka da ƙa'idojin kwansutushin.
Yayin ziyarar da ya kai Ibadan, jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde ya kara jaddada cewa dole shugaban PDP ya yi murabus kafin 2023.
Asali: Legit.ng