Babbar Matsala Ga Atiku Yayikn da Wata Ƙungiyar Yan Arewa Ta Goyon Bayan Atiku a 2023
- Gamayyar ƙungiyoyin yan arewa dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun ayyana goyon baya ga Tinubu
- Shugaban ƙungiyar, Sa'adu Yusif Dandare, ya yi alƙwarin yi wa ɗan takarar APC kamfe gida-gida a wani taro da suka gudanar
- Wannan gagarumin goyon baya na zuwa ne duk da cewa ɗaya daga cikin manyan abokan hamayyar Tinubu jigon arewa ne
Al'ummar arewa da ke zaune a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun ayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Shiyyar kudu maso yamma ta ƙunshi jihohin Legas, Ondo, Oyo, Ekiti, Osun Ogun, kuma baki ɗaya yan arewa dake waɗan nan jihohin sun mara wa APC baya.
A cewarsu, nasarar Bola Tinubu na zama shugaban ƙasa na da matuƙar amfani idan aka yi la'akari da matsalar tsaron da ake fama da ita, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sun kuma roƙi 'yan Najeriya da su zaɓi mutum mai nagarta da kwarewa ba wai Addini ba, inda suka ƙara da cewa akwai bukatar mutane su haɗa kai don taimaka wa Tinubu/Shettima su kai ga nasara tare da yan takarar gwamnonin APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ɗaukar wa Tinubu alƙawari
Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da Kamfen ɗin APC Door-to-Door, shugaban ƙungiyar yan arewa a kudu maso yamma, Sa'adu Yusuf Dandare, yace zasu tattara wa Tinubu tulin ƙuri'u.
A kalamansa yace:
"Wannan taron kaddamarwan ya ƙara wa mambobin mu kwarin guiwa da karsashi a kafatanin shiyyar (kudu maso yamma) kuma zamu kafa kwamitin dabaru nan take don fara aiwatar da salom kanfen ɗin mu na Door to Door."
"Na tsawon wannam lokacin hakan ya kasance babbar dabarar da muke amfani da ita wajen kawo wa jam'iyar mu tulin kuri'u a kudu maso yammacin Najeriya."
A wani labarin kuma Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Yi Kus-Kus da Wani Gwamnan APC
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, na jam'iyyar APC ya ziyarci tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar NNPP yace ya karɓi bakuncin gwamnan ranar Laraba da daddare a Minna.
Asali: Legit.ng