'Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan a Mutun Peter Obi da Suka Fara Gangami a Jihar Ebonyi

'Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan a Mutun Peter Obi da Suka Fara Gangami a Jihar Ebonyi

  • 'Yan a mutun Peter Obi sun fito taron gangami a jihar Ebonyi domin tara mutane sama da miliyan daya a jihar
  • Sai dai, an samu tsaiko yayin da 'yan sanda suka fatattake su tare da harba musu barkonon tsohuwa
  • Al'adar 'Obiedients' ce tara mutane a jihohi domin gangamin nuna kauna da tallata dan takarar shugaban kasa na LP

Abakaliki, Ebonyi - Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta fatattaki dandazon jama'ar da suka taru a Abakaliki a dandazon mutum miliyan magoya bayan dan takarar shugaban kasan LP, Peter Obi.

Rahoton The Nation ya ce, masoya Obi sun taru ne a Pastoral Centre dake Abakaliki, inda 'yan sanda suka fatattake su da barkonon tsohuwa.

'Yan a mutun Peter Obi sun gamu da fushin 'yan sanda
'Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan a Mutun Peter Obi da Suka Fara Gangami a Jihar Ebonyi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An ce lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin Old Enugu a birnin na Abakaliki a yau Asabar 17 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Daya daga cikin 'yan tawagar, Steve Ugama ya ce 'yan sandan sun tarwatsa tarin tare da kame mutum biyar daga abokansa, rahoton Punch.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Wannan rashin tausayi ne kuma ya saba 'yancin dimokuraɗiyya. Mun taru da safe ne din yin gangaminmi cikin kwanciyar hankali, sai kawai kwatsam, 'yan sanda suka dira suka fara harba barkonon tsohuwa a kanmu tare da kama wasu mutane.
"Sun ce ba zamu yi gangamin ba saboda gwamna David Umahi ya umarce su su hana mu, cewa ba za a yi gangamin ba. Akalla hudu daga abokan mu aka kama. Muna bukatar taimako a nan.

Sai dai, an ce daga baya an ga dandazon jama'ar sun sake taruwa a babban titin Enugu-Abakaliki.

Ku Yi Watsi da Tinubu, Atiku da Obi, Shawarin Kwankwaso Ga ’Yan Najeriya

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba 'yan Najeriya shawari kyauta, ya su kiyayi kansu su yi watsi da 'yan takarar shugaban kasa a APC, PDP da LP.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto uwa da danta da aka sace

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su zabi Bola Ahmad Tinubu, Atiku Abubakar ko Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa, Premium Times ta ruwaito.

A fahimtar Kwankwaso, ya kamata 'yan Najeriya su nisance 'yan takarar saboda basu da wani abin a zo a gani da za su iya ba kasar bayan an zabe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.