Dan Takarar Shugaban Kasan PDP Atiku, Zai Shilla Turai a Wata Tafiyar Kasuwanci
- Yanzu muke samun labarin cewa, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai tafi turai taron kasuwanci
- Makwanni uku da suka gabata ne Atiku ta daura haramar tafiyar kasuwanci, amma ya dawo don dinke barakar dake jam'iyyar
- Ana ci gaba da ganin cece-kuce da rikici a jam'iyyar PDP, lamarin da ke kara sanya shakku a zukatan magoya bayan jam'iyyar
FCT, Abuja - Awanni kadan bayan sanar da mambobin tawagar kamfen dinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023, Abubakar Abubakar zai tafi turai wani taro mai muhimmanci.
Rahoton da muka samo daga jaridar Vanguard ya ce, Atiku zai tafi turai ne domin halartar wani zama na harkallar kasuwancinsa.
Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da hadimin Atiku, Mazi Paul Ibe ya fitar ya ce mai gidan nasa zai tafi turai bayan kammala wata zama da masu ruwa da tsaki na Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) tare da abokin gaminsa, gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
Tafiyar dai zai yi ta ne a yau Juma'a 16 ga watan Satumba, kamar yadda sanarwar ta bayyana, rahoton Daily Trust.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga bakin hadimin Atiku
Paul Ibe ya ce:
"Tafiyar yau ci gaba ce ga tafiyar kasuwancin farko a makwanni 3 da suka gabata.
"A karshen tafiyar ta Turai, tsohon mataimakin shugaban kasar zai kuma yi amfani da damar don ziyartar ahalinsa a Dubai.
"Tafiya dai ta kasuwanci da kuma ganawa da ahali kuma ba ta da alaka da batun lafiya kamar yadda wasu ke yadawa."
Jam'iyyar PDP ta saki sunayen mutum 326 da za su yi aiki a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar.
A bangare guda, har yanzu akwai kura daga wasu jiga-jigan PDP da ke kira da dole shugaban jam'iyyar ya ajiye aikinsa ya ba wani.
Ku Zabi Shugabanni Masu Nagarta, Jonathan Ga ’Yan Najeriya Bayan Ganawa da IBB da Abdulsalami
A wani labarin, shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya shawaci 'yan Najeriya kan irin shugabannin da ya kamata a ce sun zaba a zaben 2023 mai zuwa.
Jonathan ya bayyana wannan batu ne a jihar Neja bayan ganawa da tsoffin shugabannin Najeriya biyu na mulkin soja Janar Badamasi Babangida Janar Abdulsalam Abubakar a birnin Minna, jihar Neja.
Da yake bayyana shawarinsa, ya ce ya kamata 'yan Najeriya su maida hankali su zabi shugabannin da za su yi aiki tukuru don kawo ci gaba a kasar nan, Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng