Shugaban Jam'iyyar APC Na Wata Jihar Arewa Ya Yi Murabus

Shugaban Jam'iyyar APC Na Wata Jihar Arewa Ya Yi Murabus

  • Alhaji Ibrahim Bilal, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na jihar Adamawa ya yi murabus daga kujerarsa sakamakon rikicin da ke faruwa a jam'iyyar
  • Majiyoyi daga jam'iyyar APC a Adamawa sun ce akwai yiwuwar an shawarci Bilal ya yi murabus ne saboda zarginsa da ake yi da hada kai da yan jam'iyyar adawa
  • Samaila Tadawus, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na Adamawa zai fara aiki a matsayin shugaban riko zuwa lokacin da kwamitin NWC za ta dauki mataki kan murabus din Bilal

Jihar Adamawa - Rikicin da ke faruwa a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Adamawa ta janyo shugaban jam'iyyar, Alhaji Ibrahim Bilal ya yi murabus.

Ya mika wasikar murabus dinsa nan take, a cewar wani rahoto na jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Yan Jam'iyyar PDP 7000 Sun Sauya Sheka APC A Jihar Sakkwato

Murabus din Bilal na zuwa ne a yayin da ake samun rashin jituwa tsakaninsa da Kwamitin Ayyuka na jam'iyyar.

Jam'iyyar APC
Shugaban Jam'iyyar APC Na Wata Jihar Arewa Ya Yi Murabus. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An zargi Bilal da hada kai da yan jam'iyyar adawa

Majiyoyi daga cikin jam'iyyar sun ce ta yi wu an bashi shawarar yin murabus ne bayan an zarge shi da hada kai da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar hammaya da wasu abubuwan.

Amma, cikin wasika mai dauke da kwanan wata na 13 ga watan Satumban 2022, da Bilal ya rubutawa shugaban APC na kasa, Sanata Abdullah Adamu ta hannnun Kwamared Mustapha Salihu, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa, shiyyar arewa maso gabas, Bilal bai bayyana dalilin murabus dinsa ba. Kawai ya ce ya yi murabus ne nan take.

Wasikar ta Bilal ta ce:

"Na rubuta wannan wasikar ne don sanar da kai cewa na yi murabus daga mukamin da aka zabe ni a matsayin shugaban jam'iyyar mu ta APC reshen Jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar PDP Za Ta Sha Kaye A Zaben Shugaban Kasa Na 2023, In Ji Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji

"Duk da cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar mu ta bukaci in tsaya a ofis har 2026, zan yi godiya, idan za a bani damar sauka daga mukamin nan take. Ina bada hakuri bisa duk wani rashin jin dadi da wannan zai janyo."

Mataimakin shugaban APC na kasa (Arewa maso gabas) ya tabbatar da samun wasikar murabus din Bilal

Kwamared Salihu, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa na arewa maso gabas, ya mika wasikar ga shugaban jam'iyya na kasa, yana mai nuna nuna cewa ya ga wasikar.

A wasikar Salihu zuwa ga shugaban jam'iyya na kasa (kwafin da aka rabawa yan jarida) ta ce:

"Bayan tuntuba da taro a mataki da dama na jam'iyya. Ina rubuta wasikar nan don sanar da kai cewa ciyaman din APC na Jihar Adamawa Alh. Ibrahim Bilat ya mika takardar murabus dinsa nan take.
"Duba da murabus din da ya yi, Samaila Tadawus (mataimakin shugaban jam'iyya) zai fara aiki matsayin shugaban rikon kwarya har zuwa lokacin da kwamitin NWC za ta dauki mataki."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo

Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari

A wani rahoton, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.

Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel