Najeriya Na Bukatar Tsarin Aikin Obasanjo, Karimcin Abacha da Jajircewar Buhari, Inji Kashim Shettima

Najeriya Na Bukatar Tsarin Aikin Obasanjo, Karimcin Abacha da Jajircewar Buhari, Inji Kashim Shettima

  • Tsohon gwamnan Borno, kuma abokin Bola Ahmad Tinubu na APC, Kashim Shettima ya bayyana kadan daga dabi'un abokin takararsa
  • Shettima ya ce Najeriya na bukatar shugaba mai dabi'u uku daga shugabannin Najeriya don iya rike kasar da kyau
  • Gwamnan jihar Legas ya amince da batun Shettima, ya ce Tinubu ne ya cancanci gaje kujerar shugaba Buhari

Ikoyi, Legas - Abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana abubuwan da kasar nan ke bukata daga shugaban da zai gaji Buhari a 2023 don kawo ci gaba a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Da yake magana ranar Alhamis 15 ga watan Satumba bikin murna na 96 na kungiyar Yoruba Tennis Club da aka yi a Ikoyi ta Legas, Shettima ya ce Tinubu dan takarar da ya cika abin da ake bukata.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Shettima ya bayyana Tinubu ya halin shugabannin Najeriya uku
Najeriya Na Bukatar Tsarin Aikin Obasanjo, Karimcin Abacha da Jajircewar Buhari, Inji Kashim Shettima | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewar Shettima, Bola Ahmad Tinubu na jam'iyyar APC ne ya cika duk wasu abubuwan da ake bukata daga shugaban da ya cancanci hawa kujerar mulkin Najeriya.

Ya kuma ce, Tinubu da karimci irin na tsohon shugaban Najeriya Sani Abacha da kuma jajircewa kamar na shugaban Najeriya na yanzu, Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu na da hali irin na Obasanjo, inji Shettima

Baya ga wadannan, ya ce Tinubu na da tsarin aiki irin na tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, rahoton TheCable.

A cewarsa:

“A ‘yan kwanakin nan, mun ga yadda abubuwa ke dagulewa game da rashin yarda da ra’ayin hadin kan kasa. Gaskiyar magana ita ce, gina kasa aiki ne da ya kamata ya ci gaba, kuma dole ne mu ci gaba da kyautata zaton samun haka."

Hakazalika, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu yace tabbas Tinubu ne dan takarar da ya cancanci ci gaba da aiki daga inda shugaba Buhari ya tsaya.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi

Buhari Ya Ba Amurkawa, ’Yan Birtaniya da Sauran Kasashe Takardar Zama ’Yan Najeriya

A wani labarin kuma, a Alhamis 15 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa mutum 286 'yan kasar waje takardar shaidan zama ‘yan Najeriya.

Rahoton Daily Trust ya ce, mutanen sun fito ne daga kasashen Birtaniya, Amurka, Siriya, Lebanon, Falasdinu, Masar da Italiya.

Mutum 208 daga cikinsu an ba su takardar shaidar zama asalin ‘yan kasa yayin da sauran 78 kuma suka samu takardar shaidar zama dan Najeriya ta hanyar rajista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.