Ku Zabi Shugabanni Masu Nagarta, Jonathan Ga ’Yan Najeriya Bayan Ganawa da IBB da Abdulsalami
- Tsohon shugaban Najeriya ya shawarci 'yan kasar kan irin shugaban da ya kamata a zaba a zaben 2023 mai zuwa
- Goodluck Jonathan ya fadi haka ne bayan ganawa da wasu tsoffin shugabannin kasar nan a jihar Neja
- Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da tallata 'yan takararsu a daidai lokacin da zabe ke kara gabatowa
Minna, jihar Neja - Shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya shawaci 'yan Najeriya kan irin shugabannin da ya kamata a ce sun zaba a zaben 2023 mai zuwa.
Jonathan ya bayyana wannan batu ne a jihar Neja bayan ganawa da tsoffin shugabannin Najeriya biyu na mulkin soja Janar Badamasi Babangida Janar Abdulsalam Abubakar a birnin Minna, jihar Neja.
Da yake bayyana shawarinsa, ya ce ya kamata 'yan Najeriya su maida hankali su zabi shugabannin da za su yi aiki tukuru don kawo ci gaba a kasar nan, Vanguard ta ruwaito.
Hakazalika, ya ce ya kamata a duba shugabannin masu inganci da kuma tarihi mai kyau don haifar da da mai ido a lokacin mulkinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce ta haka ne kadai Najeriya za ta samu shugabanni nagari da za su iya kawo sauyi mai amfani da ci gaba a kasar.
Irin shugaban da ya kamata 'yan Najeriya su zaba a 2023
A bangare guda, ya ce bai kamata 'yan Najeriya su zabi shugaban da zai dauki bukatun kansa fiye da na kasa ba a zaben 2023, rahoton Punch.
A cewarsa:
"Duk muna yiwa kasarmu fatan alheri. Ga 'yan Najeriya baki daya, musamman matasa, zabe na nan tafe.
"Ya kamata su zabi shugaban da suka san zai jagorance mu da kyau, mutumin da zai mana aiki tukuru.
"Jagora bawa ne kuma shugaban jama'a, kai za ka jagoranta kuma kai za ka shugabanta.
Ku zabi shugaban da zai dauki bukatunmu gaba daya, bukatun kasa, mutumin da ba zai dauki bukatunsa sama da bukatunmu ba da na kasa.
"Mutumin da zai tafi tare damu gaba daya, musamman ma mutumin da zai dauki Najeriya a matsayin wani aiki na musamman."
Jonathan Ya Yi Wata Ganawar Sirri da IBB, Abubakar a Birnin Minna, Jihar Neja
A wani labarin, tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kai wata ziyarar kai da kai ga tsoffin shugabannin soja; Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar a birnin Minna ta jihar Neja.
Tsohon shugaban ya gana da tsoffin shugabannin na soji ne a gidajensu da yammacin yau Alhamis 15 ga watan Satumba, Vanguard ta ruwaito.
Da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida, Goodluck ya ce ya kawo ziyarar ne kamar yadda ya saba ga tsoffin shugabannin.
Asali: Legit.ng