Bola Tinubu Ya Shiryawa su Atiku, An Kafa Kwamitocin da Za Su Taimaka Masa a Kudu

Bola Tinubu Ya Shiryawa su Atiku, An Kafa Kwamitocin da Za Su Taimaka Masa a Kudu

  • Rotimi Akeredolu da Adeniyi Adebayo ne za su shugabanci kwamitocin neman zaben APC a Kudu maso yamma
  • Jam’iyyar APC ta zabi wadanda za su dage wajen ganin Bola Tinubu ya kai labari a zaben shugabancin Najeriya
  • Isaac Kekemeke ya bada wannan sanarwa, yace ‘yan kwamitin sun hada da Iyiola Omisore da Yetunde Adesanya

Oyo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Adeniyi Adebayo, za su jagoranci yakin zaben Asiwaju Bola Tinubu.

Premium Times tace wadannan ‘yan siyasa za su jagoranci kwamitocin da jam’iyyar APC ta kafa a kudu maso yamma domin zaben shugaban kasa a 2023.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto cewa wadannan kwamitoci za su agazawa ‘dan takaran APC watau Bola Tinubu a yankinsa da nufin lashe zaben badi.

Mai girma Rotimi Akeredolu shi ne shugaban kwamitin tattaunawa da manyan mutane, Niyi Adebayo zai rike shugabancin kwamitin bada shawara.

Rahoton da muka samu shi ne Adebayo za iyi aiki a wannan kwamitin tare da Pius Akinyelure.

Ragowar 'yan kwamiti

Sauran ‘yan wannan kwamiti sun kunshi sakataren APC na kasa, Iyiola Omisore da Olubunmi Oriniowo, sai Yetunde Adesanya da shugabar matar jam’iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu, Simon Lalong da Abdullahi Ganduje Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Duka shugabannin APC na jihohin Legas, Oyo, Ogun, Ondo, Osun da Ekiti suna cikin kwamitin.

Ragowar ‘yan kwamitin da za suyi aiki da Akeredolu domin kai APC ga nasara su ne: Tajudeen Olusi, Bamidele Oluwajana, Henry Ajomale da Vincent Bewaji.

Aikin da ke gaban mu - Isaac Kekemeke

The Nation ta rahoto mataimakin shugaban APC na shiyyar Kudu maso yamma, Isaac Kekemeke yana cewa an kafa kwamitocin domin cin zaben 2023.

Da yake bayani a Ibadan, Kekemeke yace kwamitocin za su yi aiki ne a kudancin kasar.

A cewarsa, za su yi bakin kokarinsu wajen ganin cewa abin da ya faru da Obafemi Awolowo da Marigayi MKO Abiola bai sake faruwa da Bola Tinubu ba.

Okowa ya fi dacewa - Ayu

Kun samu labari abubuwan da ham'iyyar PDP ta duba wajen zakulowa Atiku Abubakar wanda ya dace da shi a takarar 2023, har da ilmi da kokari a ofis.

Shugaban PDP na Najeriya, Dr. Iyorchia Ayu yace jam’iyyar PDP ta yaba da saukin kan Dr. Ifeanyi Okowa, wannan ne ya sa aka ki daukar Gwamna Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel