Yan Sanda Sun Kama Dan Takarar Sanatan PDP Kan Takardun Jabu
- Jami'an yan sanda sun cafke ɗan takarar Sanatan Bayelsa ta tsakiya, Hon. Friday Konbowei Benson, kan zargin amfani da takardun bogi
- Benson, tsohon Sakataren gwamnatin jihar Bayelsa, ya samu nasarar zama ɗan takarar Sanata ne bayan lallasa wanda ke kan kujerar
- Kwamishinan yan sandan Bayelsa yace ya fahimci zuwan tawagar IGP jihar, amma bai san abinda ya kawo su ba
Bayelsa - Dakarun yan sandan Najeriya sun kama tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Bayelsa kuma ɗan takarar Sanatan Bayelsa ta tsakiya a inuwar PDP, Hon. Friday Konbowei Benson kan zargin gabatar da takardun jabu.
Leadership tace Benson, tsohon Sakataren gwamnatin Bayelsa da bai jima da sauka ba, ya samu nasara a zaɓen fidda gwanin PDP ta hanyar lallasa Sanata mai ci, Moses Cleopas.
Mista Benson ya samu kuri'u 110 da suka ba shi damar zama zakara a zaɓen kuma ya kayar da Honorabul Cleopas, wanda ya tashi kuri'u 22 kacal.
Sai dai lamarin bai wa Sanata Cleopas daɗi ba, ya koka kan yadda aka shirya zaɓen fidda gwanin, daga bisani ya maka Benson a gaban babbar Kotun tarayya dake zama a Yenagoa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A karar, Sanatan mai ci ya zargi wanda ya lashe zaɓen da gabatar wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) takardun shaidar karatu na bogi.
Legit.ng Hausa ta gano cewa dakaru na musamman na Ofishin Sufeta Janar na ƙasa a ranar Laraba sun dira Yenagoa, babbam birnin jihar Bayelsa domin kame Benson.
Bayanai sun ce sun tasa shi zuwa sashin binciken aikata manyan laifuka na jiha (SCID) inda ya amsa tambayoyi kuma suka ɗauki bayanansa.
Kwamishina Yan sanda ya samu labari
Kwamishinan yan sandan Bayelsa, Ben Okolo, wanda ya tabbatar da zuwan tawagar IGP, yace bai da masaniya kan maƙasudin Kes ɗin da suke aikin bincike a jihar.
Haka zalika da aka tuntuɓe shi, Sanata Cleapas, ya musanta ƙulla kama abokin hamayyarsa, inda yace:
"Yan sandan Najeriya ba ƙarƙashina suke ba, dan haka bani da hurumin shiga aikinsu. Suna gudanar da aikinsu ne yadda ya dace."
A wani labarin kuma Dubun Wani Kwararren Likita Dake Kashe Mutane Da Allura Don Sace Motocinsu Ya Cika
Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Edo sun kama wani kwararren Likita dake kashe Direbobi don ya sace Motocinsu.
Kakakin hukumar yan sanda, SP Nwabuzor, yace Likitan mai suna, Abbas Adeyemi, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Asali: Legit.ng