Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi
- Jigon jam'iyyar APC, Prince Tajudeen Olusi, ya yi shagube ga masu yiwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba'a kan lafiyarsa
- Olusi ya ce kowani mutum na da irin nasa lalurar da ke damunsa hatta shi karan kansa, cewa Tinubu na da lafiya tunda yake iya zagaye kasar ba tare da ya kai kasa ba
- Tsohon dan majalisar na jumhuriya ta biyu ya ce da izinin Allah dan takarar na APC zai lashe zaben shugaban kasa a 2023
Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Prince Tajudeen Olusi, ya gargadi masu zolayar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, kan lafiyarsa.
Olusi ya bayyana cewa babu wani dan adam da baya da wata matsala ta rashin lafiya da ke damunsa a rayuwa.
Da yake jawabi a wata hira da jaridar Daily Independent a ranar Talata, Olusi, ya ce duba da yadda Tinubu ke yawo a fadin kasar tun bayan da ya lashe tikitin APC ba tare da ya kwanta ba ya nuna babu abun da ya samu lafiyarsa.
Tsohon dan majalisar wakilan na jumhuriya ta biyu ya ce Tinubu zai kunyata masu sukarsa ta hanyar kamfen a fadin kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma ce tsohon gwamnan na Lagas zai lashe zaben shugaban kasar sannan a rantsar da shi a ranar 19 ga watan Mayun 2023.
Jaridar ta nakalto Olusi yana cewa:
“Kowani mutum yana da nashi kason na rashin lafiya. Ni, yanzu haka da nake magana da ku, ina da nawa rashin lafiya da nake kula da su a yanzu. Haka abun yake ga mutane da dama.
“Ga wadanda suke magana game da rashin lafiyar Asiwaju, a nan mutum ne wanda ya jagoranci jihar Lagas tsawon shekaru takwas a matsayin gwamna. Baya ga haka, ya yi shugabancin jam’iyya tun bayan da aka kafa APC har zuwa yanzu.
“Mutumin na ta yawo daga wannan bangare zuwa wancan bangaren na kasar tun bayan da ya lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC amma kuma har yanzu bai kwanta ba koda kuwa na rana daya ne.
“Da izinin Allah zai ci gaba da kamfen, ya shiga zabe, za mu lashe zabe kuma a gaban dukkan mu, za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya. Don haka, bu bar batun rashin lafiyarsa da sauran abubuwa a hannun Allah.”
2023: Dogara Da Babachir Sun Gana Da Kiristocin Arewa Don Kalubantar Gamin Tinubu Da Shettima
A wani labarin, mun ji cewa manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hon. Yakubu Dogara da Babachir David Lawal, suna ci gaba da nuna rashin gamsuwarsu a kan tikitin Musulmi da Musulmi, cewa za su ci gaba da fafutuka don ganin an yi adalci.
Dogara, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai, shine ya bayyana hakan bayan ganawarsu da shugabannin kiristoci daga jihohin arewa 19 da babbar birnin tarayya a ranar Talata.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya kasance Musulmi shine dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023, inda jam’iyyar ta sake zakulo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima wanda shima Musulmi ne don ya zama abokin takararsa.
'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Fitaccen Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP
Asali: Legit.ng