Yadda Mambobin APC da PDP Zasu Yi Watsi Da Tinubu, Atiku a Zaben 2023, Jigon LP
- Jigon jam'iyyar Labour Party, Victor Umeh, yace akwai wasu mambobin APC da PDP da zasu zaɓi Peter Obi a zaɓen 2023
- Umeh, wanda ke neman kujerar Sanata daga jihar Anambra, yace mutane sun gano cewa LP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya
- A ranar Litinin da ta gabata, ƙungiyar kwadugo ta ƙasa ta ayyana goyon bayanta ga Peter Obi na jam'iyyar LP
Jigon jam'iyyar Labour Party (LP), Victor Umeh, ya yi ikirarin cewa wasu jam'iyyun siyasa ciki har da APC da PDP na takaicin yadda 'yan Najeriya ke ƙara karɓan LP a faɗin ƙasar nan.
Ɗan takarar Sanata daga jihar Anambra a inuwar jam'iyyar LP yace wasu mambobin APC da PDP lokaci kawai suke jira, zasu dangwala wa Peter Obi ƙuri'unsu a zaɓe mai zuwa.
Umeh ya yi wannan furucin ne ranar Laraba a shirin karin kumallo na kafar Talabijin din Channels TV mai suna, 'Sunrise Daily.'
"A yanzun batun ya zarce a ina kake, na san cewa akwai 'ya'yan jam'iyyar PDP da zasu zaɓi LP. Abinda aka sanya a gaba shi ne ceto Najeriya kuma mutane sun yi imanin cewa LP ce kaɗai zata iya."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Victor Umeh
Ƙungiyar NLC ta mara wa Obi baya
Shugaban ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC), Ayuba Wabba, ranar Litinin a Abuja, yace ƙungiyar tare da sauran masu haɗa kai da ita zasu tara wa Obi kuri'u miliyan 12m a zaɓen shugaban kasan 2023.
Da yake tsokaci kan kalaman Wabba, Umeh yace NLC na da karfin haɗa wa Peter Obi tulin kuri'u, "Saboda ƙungiya ce mai tsari," kuma ƙungiyoyi na cikin tsaka mai wuya a yanzu.
"Mutane na maƙale da jam'iyyar Labour Party, duba yadda lamari ke tafiya a Najeriya a faɗin sassan jihohin ƙasar nan. Idan kace LP bata da ƙarfi a wasu yankuna sai kasha mamaki. Mutane ne karfin LP."
Ta ya Peter Obi zai ja ra'ayin yan arewa:?
Game da yadda ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP zai mamaye zuƙatan 'yan arewa, Umeh yace, "Yana cigaba da tattaunawar neman shawari, Obi na ɗaya daga cikin 'yan takarar da ke karaɗe shiyyoyi don neman shawari."
A wani labarin kuma Wani Gwamnan APC Ya Faɗi Wanda Yake Kaunar Ya Gaji Buhari a 2023 baya ga Bola Tinubu
Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, yace tafiyar Peter Obi ta ƙara nuni da cewa Kudu maso gabas ba abin jefarwa bane a harkokin siyasar Najeriya.
Jim kaɗan bayan gana wa da Buhari a Abuja, Umahi yace idan aka ɗauke Tinubu, to zai so Peter Obi na ɗare kujerar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng