Abin da Ya Sa Atiku Ya Yi Watsi da Wike, Ya Jawo Okowa Ya Zama Mataimakinsa
- Shugaban Jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu ya yi bayanin yadda Ifeanyi Okowa ya samu takara a zaben 2023
- Dr. Ayu yace ilmi da saukin kai suna cikin abubuwan da ya sa Atiku Abubakar ya tafi da Gwamna Okowa
- Ana tunanin daukar Gwamnan na Delta da Atiku ya yi, yana cikin dalilin rikicinsa da Gwamna Nyesom Wike
Abuja – Tun tuni abubuwa suka yi tsami a PDP tsakanin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu da kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Vanguard ta rahoto shugaban jam’iyyar ta PDP yana bayanin abin da ya sa Alhaji Atiku Abubakar ya amince Ifeanyi Okowa ya zama abokin takararsa.
Atiku Abubakar ya zabi Ifeanyi Okowa a maimakon Nyesom Wike wanda ya nemi tikitin shugabancin kasa a PDP, amma bai iya doke Wazirin Adamawa ba.
Sanata Iyorchia Ayu yake cewa Gwamna Okowa ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 ne saboda irin saukin kai da yake da shi.
A cewar shugaban jam’iyyar, baya ga saukin kai na Okowa, yayi ayyukan yabawa a kujerar gwamna jihar Delta a shekaru bakwai da ya yi yana mulki.
Okowa ya fi cancanta
Rahoton da muka samu daga jaridar Punch yace shugaban jam’iyyar ya yi ikirarin gwamnan Delta ya fi kowa dacewa da ya rike wannan kujera a PDP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Ayu ya zo ne yayin da yake magana a wajen wani taron majalisar kiristocin matasan Arewacin Najeriya wanda ake shiryawa a garin Abuja.
“Mun duba da kyau, sai muka yi tunanin akwai bukatar mu nemawa Atiku wanda zai tamaka masa, kuma muka zabi wanda yake da ilmi da kyau…
Wanda yake da saukin kai, kuma ya yi kokari a matsayinsa na gwamna a jiharsa.
Okowa shi ya fi cancanta da zama abokin takara. La'akari da dacewarsa ne jam’iyya ta zabe shi a matsayin ‘dan takarar mataimaki ga Atiku.
Ina tunanin Najeriya tayi sa’a idan wadannan mutane biyu masu son cigaba, marasa nuna kabulaci, masu imani da Najeriya suka samu mulki.
Manufofin Atiku sun fito
Da ya je Legas, an ji labari cewa ‘Dan takaran PDP na zaben shugabancin kasa, Atiku Abubakar ya yi bayanin yadda zai farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Idan gwamnatin tarayya ta koma hannun Wazirin Adamawa, za a cire tallafin man fetur, a bunkasa MSME, sannan a rage facaka da yawan cin bashi da ake yi.
Asali: Legit.ng