Wadanda Ya Kamata Su Tallata Gwamnatina Ba Sa Yin Hakan, Inji Shugaba Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kadan daga nasarorin da ya samu tun bayan hawansa mulkin Najeriya
- Buhari ya ce akwai wadanda su ya kamata suke fadin irin nasarar da ya samu, amma abin takaici basa fadi
- Najeriya ta shiga wani yanayi na yawan karbar rancen kudi daga waje tun bayan hawan Buhari a 2015
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Imo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai wadanda su ya kamata su ke tallata nasarorin da gwamnatinsa ta samu, amma sam ba sa yin hakan, TheCable ta ruwaito.
Buhari ya bayyana haka ne a yau Talata 13 ga watan Satumba a wata ziyarar bude ayyuka da ya kai jihar Imo ta kudancin Najeriya.
Shugaban ya ce, idan aka yi duba cikin tsanaki da irin albarkatun kasa da gwamnatinsa ta samu, za a fahimci irin kokarin da ya yi a mulkinsa.
Da yake tsokaci game da wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta, Buhari ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Game da batun rashin tsaro da ‘yan bindiga, gadar Neja ta biyu, idan ‘yan Nijeriya za su iya tunawa; duk da haka, magana ta gaskiya, ina zargin manyan Najeriya da rashin zama tare da yin tunani mai zurfi game da kasarmu.”
A bangare guda, shugaba Buhari ya kirayi 'yan Najeriya da su yi tunani tare da kwatanta gwamnatinsa da gwamnatocin da suka shude kafin zuwansa.
Abubuwan da gwamnatin Buhari ya cimma, daga bakinsa
Da yake bayyana kadan daga nasarorinsa, Buhari ya ce ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da kawar 'yan ta'addan Boko Haram, gina layin dogo da tituna a Najeriya.
A bangare guda, gwamnatin Najeriya a yanzu na cikin wani yanayi na tarin bashi, lamarin dake kara ruruwa wutar martani daga masu sharhi a kasar nan, rahoton People Gazette.
Ya zuwa yanzu, ana bin gwamnatin Najeriya bashin akalla N41tr, kuma galibi a karkashin mulkin Buhari aka runtumo bashin.
Hakazalika, gwamnatin a yanzu tana shirin karbo rancen kudin da ya kai N11tr domin tabbatar da tafiyar kasafin kudin 2023 yadda ake so.
Zan Cire Najeriya Daga Kungurmin Duhu Idan Na Gaji Buhari, Inji Dan Takarar PDP Atiku
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin fidda Najeriya Najeriya daga kungurmin duhun da take ciki idan aka zabe shi a zaben 2023.
Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta 2022 da aka yi a Legas, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma shawarci 'yan Najeriya da cewa, kada su rudu da siyasar farfaganda da barbade a kafafen Facebook, Twitter da Instagram, inda yace hakan ba zai kare su da komai ba.
Asali: Legit.ng