Rikicin PDP: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Wike
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Sam Ohuabunwa, ya goyi bayan fafutukar da gwamnan Ribas ke yi
- Mista Ohuabunwa ya bayyana cewa Wike na kokarin tabbatar da adalci da daidaito ne a jam'iyya kuma kowa ya san an tafka kuskure
- Gwamna Wike ya shiga takun saƙa da jam'iyyar PDP ne bayan ayyana Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban kasa
Abuja - Jigon jam'iyyar PDP, Sam Ohuabunwa, yace Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ba neman rikici yake ba, yana fafutukar ganin an yi adalci ne da daidaito amma ba kokarin wargaza jam'iyya yake ba.
Mista Ohuabunwa ya yi wannan furucin ne yayin da ya bayyana a cikin shirin 'Sunrise Daily' na kafar Talabijin Channesl tv ranar Talata.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta tsunduma cikin rikici tun bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a watan Mayu.
Gwamna Wike na ɗaya daga cikin yan takarar Tikitin PDP, ya sha kaye hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake nuna fushinsa ga zaɓen fidda gwanin, Wike ya zargi jam'iyya da yaudara da kuma karya kwansutushin ɗinta. Daga nan ya buƙaci shugaban PDP na ƙasa ya sauka, sharaɗin da sai an cika zai mara wa Atiku baya.
Duk da shugaban BoT ya sauka daga kujerarsa domin martani kan zargin rashin daidaito, Wike ya jaddada cewa dole Ayu ya yi murabus idan har ana son zaman lafiya a PDP.
Ohuabunwa, wanda ya yi ikirarin cewa yana tattauna wa da ɓangaren Wike da Atiku, ya jaddada cewa gwamnan Ribas na kokarin ganin an gyara kuskuren da aka yi a baya.
The Cable ta ruwato Ohuabunwa na cewa:
"Maganar gaskiya Wike ba kukan wofi yake yi ba, bukatarsa a yi adalci kuma a yi daidaito, kuma abu ne mai kyau ya yi haka."
Mista Ohuabunwa, tsohon ɗan takara da ya nemi tikitin shugaban ƙasa a PDP, ya roki uwar jam'iyya ta ƙasa ta duba buƙatun da gwamnan ya nema.
"Meyasa kowa ke dibar ƙafa zuwa wurin Wike? Alama ce ta yana da gaskiya a lamarin nan. Akwai abinda kowanen mu ya san kuskure ne kuma hakan ne yasa 'yan adawa ke zuwa wurinsa."
Yadda za'a warware rikicin
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya nuna yaƙinin cewa wannan rikicin zai zama tarihi daga lokacin da jam'iyyar PDP ta fahimci ainihin batun.
"Bana tunanin Wike na da wahalar sha'ani. Ina tunannin jam'iyya ta fahimci inda aka ketare layi a rikicin kuma da alamu PDP ta tashi tsaye don kada rikicin nan ya daƙushe damarta na lashe zaɓe."
A wani.labarin kuma Atiku Na Kokarin Rarrashin Wike, Wani Babban Jigon PDP Ya Koma APC a Kebbi
Yayin da ake shirin fara kamfe a karshen Satumba, babban jigon PDP a jihar Kebbi, Alhaji Jinaidu Wasagu, ya koma APC.
Wasagu yace ya tattaro zaɓaɓɓun shugabanni da tsofaffi na PDP sun sauya sheka, a bayaninsa akwai dumbin mambobi da zasu biyo baya.
Asali: Legit.ng