2023: Gumi Ya Bawa Peter Obi Muhimmin Shawara Idan Har Yana Son Ya Kai Labari A Babban Zabe

2023: Gumi Ya Bawa Peter Obi Muhimmin Shawara Idan Har Yana Son Ya Kai Labari A Babban Zabe

  • Sheikh Ahmad Gumi, babban malamin addinin islama mazaunin Kaduna ya tofa albarkacin bakinsa kan salon siyasar Peter Obi dan takarar LP
  • Gumi ya ce Obi siyasar yanki ya ke yi kuma idan har bai canja ba hakan ba zai kai shi ga nasara ba domin dan siyasa na bukatar goyon bayan dukkan kasa ba yanki guda ba kawai
  • Malamin ya kuma kara da cewa Najeriya na bukatar kwararren dan siyasa a matsayin shugaban kasa, yana mai cewa Peter Obi ba kwararre bane idan aka kwantata shi da Tinubu da Atiku

Kaduna - Malamin addini mazaunin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya zargi dan takarar shugaban kasar jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi da yin siyasar yanki, rahoton The Nation.

Ya ce irin wannan salon siyasar ba zai haifar wa Obi da mai ido ba.

Kara karanta wannan

Abdullahi Haske: Matashin Biloniya Daga Jihar Adamawa Wanda Ba Kowane Ya Sansa Ba

Peter Obi da Gumi
2023: Sheikh Gumi Ya Yi Fashin Bakin Kan Salon Siyasar Peter Obi. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Gumi, wanda ya yi magana da yan jarida kan zaben 2023 da halin da kasa ke ciki a gidansa, ya ce Najeriya na bukatan kwararen dan siyasa ya fitar da ita zuwa tudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya, a cewarsa, ba ta bukatar dan koyo a matsayin shugaban kasa.

Ya ce akasin Obi, dan takarar APC, Asiwaju Bola Tinubu da na PDP, Atiku Abubakar suna da kwarewar da aka bukata don jagorancin kasar.

A cewarsa:

"Najeriya na bukatar kwararren dan siyasa. Ba mu bukatar don koyo ya zama shugaban kasa. Halin da ake ciki a Najeriya yanzu na bukatar kwararen dan siyasa ya warware ta."

A kan Obi, ya ce:

"Matasan da ke goyon bayansa sun rabu kamar manya. Yana da bukatar ya tuntubi sauran sassan Najeriya. Dogara da matasa kawai ba zai isa ba. Ya kamata ya shiga ko ina ba wai ya takaita siyasar a yanki guda ba kawai."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Buhari Baya Kaunar Najeriya Yadda Nake Sonta

Sheikh Gumi ya shawarci yan Najeriya kan zaben 2023

Malamin ya shawarci yan Najeriya su yi watsi da siyasar addini da kabilanci a siyasar zamanin yanzu na karni na 21 su hada kai don kawo cigaba.

Ya yi gargadin cewa idan aka zabi dan siyasar da bai kware ba, zai gaza zabo hazikai cikin lokacin da ya dace don kawo cigaba a a kasar.

Gumi ya ce Buhari ya shafe wata shida kafin ya nada ministoci saboda a lokacin shi ba kwararren dan siyasa bane.

Wani sashi na jawabinsa:

"Mu yi magana kan hada kan mutanen Najeriya. Babu wanda ke da iko da wani a kasar. Don haka mu nemi cigaba. Duba Amurka, babu wanda ke maganar karba-karba. Mu gina demokradiyya da za ta dore."

2023: Duk Wata Boye-Boye Ta Zo Karshe, An Gano Dan Takarar Da Obasanjo Zai Mara Wa Baya

A bangare guda, kakakin kamfen din Atiku Abubakar, Charles Aniagwu ya jadada cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai goyi bayan mai gidansa a zaben 2023.

Da ya ke magana da yan jarida a Asaba a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba, Aniagwu ya ce Obasanjo ya san kwarewa ca cancantar Atiku saboda ya taka muhimmin rawa wurin daidaita tattalin arzikin Najeriya daga 1999 zuwa 2007, PM News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164