Sheikh Gumi: Buhari Baya Kaunar Najeriya Yadda Nake Sonta

Sheikh Gumi: Buhari Baya Kaunar Najeriya Yadda Nake Sonta

  • Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmed Gumi, ya sanar da cewa ya fi shugaba Buhari kaunar kasar nan
  • Malamin ya sanar da hakan yayin da yake wa'azin mako-mako a masallacin Sultan Bello dake Kaduna inda yayi martani kan kamen Mamu
  • Gumi yace ya fi kaunar kasar nan fiye da da shugaban kasa don bashi da wata kasa da ta wuce Najeriya, hakan yake fatan samuwar zaman lafiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Sheikh Ahmed Gumi yace shugaban kasa Muhammadu Buhari baya son kasar nan kamar yadda yake kaunarta.

Gumi yace hakan yayin martani kan kamen Tukur Mamu wanda jami'an tsaron farin kaya suka cafke, Daily Trust ta rahoto.

Baba Buhari
Sheikh Gumi: Buhari Baya Kaunar Najeriya Yadda Nake Sonta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wa'azinsa na mako-mako a masallacin Sultan Bello dake Kaduna, Gumi yace ya dace gwamnati ta bai wa Mamu hakuri kan yadda ta tsorata shi tare da firgita shi.

Kara karanta wannan

Kama Tukur Mamu: Babu bambanci tsakanin gwamnati da 'yan ta'adda, Sheikh Ahmad Gumi

Yace shi da kan shi ya bi hanyar kwantarwa da 'yan bindiali domin a samu zaman lafiya, amma wasu mutanen basu son gaskiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A matsayinmu na mutane, ba za mu kalmashe hannuwanmu ba mu yi shiru. Na san ayyukan tsaro saboda na taba shiga tsarin da kaina. Don haka na san yadda suke aiki kgan hankuma na san hadin bakinsu.
"Ko Sardauna bai kubuta daga kutunguila ba, kamar yadda Murtala, Maimalari, IBB da shi kanshi Buhari. Kowanne ya sha wahalar hakan.
“A cikin kwanakin nan, Malam Goni ya fada tarkonsu inda wasu sojoji suka kashe shi. Amma waye ke alfahari da su? Na yanke hukuncin shiga lamarin ne domin samo wa kasar nan daidaituwar zaman lafiya."

- Sheihin Malamin yace.

"Bari in fada muku ko shugaban kasa baya kaunar kasar nan kamar yadda nake yi saboda bani da wata kasa baya da Najeriya.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

“Ina son kasar nan ta kasance cikin kwanciyar hankali wanda saboda sun gane da gaske nake suka yanke hukuncin kirana da kowanne irin suna tare da alakanta ni da ta'addanci.
"Abinda ya fusata ni lokacin da nace mutanen sun cancanci abubuwan more rayuwa kamar asibitoci, makarantu kamar yadda aka yi wa tsagerun Nuger Delta. Hakan ya janyo min zagi."

Gumi ya kara da cewa.

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

A wani labari na daban, Tukur Mamu, mawallafi kuma mazaunin Kaduna an kama shi a Cairo sakamakon zarginsa da ake da hannu wurin karbar kudin fansa tare da kai wa 'yan ta'adda domin sakin wadanda suka sace, Daily Trust ta tattaro daga majiya mai karfi.

Daily Trust ta rahoto cewa, wasu majiyoyin tsaro sun ce baya ga alaka da 'yan ta'addan Najeriya, Mamu ya shiga hannun hukuma ne saboda alakar da yake da ita mai karfin da wata kungiyar ta'addanci a yankin Sinai dake Misra.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta

Sinai Peninsula yankin arewa maso gabas ne na Misra da ya hada Isra'ila da Gaza ta gabas. Kamar a Najeriya, duk da raguwar yawan hare-haren ta'addanci, 'yan ta'afddan suna nan a yankin kuma sun zama babbar barazana ga jami'an tsaro da sauran Sinai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel