2023: Ba Wanda Zan Janye Wa Takarar Shugaban Kasa, Kwankwaso

2023: Ba Wanda Zan Janye Wa Takarar Shugaban Kasa, Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta rahoton dake cewa yana duba yuwuwar janye wa Atiku ko Tinubu
  • Mai magana da yawun tawagar kanfen din Kwankwaso, Ladipo Johnson, yace ya kamata yan Najeriya su daina ɗaukar kowake zance
  • Johnson yace NNPP ta shirya fara yaƙin neman zaɓe kuma zata karaɗe duk sassan Najeriya don tallata manufofinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Ladipo Johnson, mai magana da yawun tawagar yaƙin neman zaɓen Sanata Rabiu Kwankwaso, a 2023, ya yi watsi da raɗe-raɗin dake yawo cewa ɗan takarar NNPP zai janye ya mara wa wani baya.

Johnson ya maida martani kan rahoton dake yawo a kafafen sada zumunta cewa wai ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP mai kayan daɗi na duba yuwuwar janye wa Atiku ko Tinubu.

Atiku Abubakar tare da Rabiu Kwankwaso.
2023: Ba Wanda Zan Janye Wa Takarar Shugaban Kasa, Kwankwaso Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa a wata sanarwa da ya fitar a Legas ranar Lahadi, Johnson, ya bayyana cewa Kwankwaso ya shiga tseren ne domin ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Zaɓi Biyu Da Ya Rage Wa Mutane a 2023

"Ban san meyasa mutane ke zama su kirkiri irin waɗannan raɗe-raɗin marasa tushe ba, Kwankwaso ba zai taɓa janye wa wani takararsa ta shugaban kasa ba," Inji Johnson.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa Kwankwaso ya shiga tseren gaje Buhari?

Kakakin Kamfe ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Kano zai gwabza a zaɓen shugaban kasan 2023 har zuwa ƙarshe domin ya shiga tseren ne da niyya mai kyau ta kawo canji a Najeriya.

"Kwankwaso bai shiga tseren takara domin ya zauna tattaunawar haɗa kai da wani ba. Yana da goyon baya da tarihin nagarta da zai jagoranci Najeriya zuwa babban matsayi."
"Babu dalilin da ɗan takarar mu zai janye, damar da yake da ita ta samun nasara tana da girma. Eh zai fafata amma yana damar lashe zaɓen idan muka yi la'akari da yadda mutane suka karɓe shi a dukkan sassan kasa."

Kara karanta wannan

Rikici Ya Girma: Jam'iyya Ta Kori Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Zaɓen 2023

Johnson ya jaddada cewa NNPP ta shirya fara kamfe kuma zata karaɗe sassan Najeriya domin jawo hankalin yan Najeriya da musu bayanin dalilin da yasa ya dace su zaɓi NNPP.

A kalamansa, ya ƙara da cewa lokaci ya yi da 'yan Najeriya zasu daina yarda da shaci faɗin kafafen sada zumunta. Yace lokacin kamfe ya kusa, zaka ga ƙarerayi kala-kala, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnan Gombe Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa, Ya Faɗi Yadda Zasu Kifad Da Atiku a Arewa

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, yace Atiku zai sha ƙasa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, ya fito daga jihar Adamawa, ɗaya daga jihohin shiyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262