Kano 2023: Jam'iyyar ADP Ta Su Rarara Ta Kori Dan takarar Gwamna Kan Abu Guda

Kano 2023: Jam'iyyar ADP Ta Su Rarara Ta Kori Dan takarar Gwamna Kan Abu Guda

  • Jam'iyyar ADP ta ƙasa ta kori tsohon ɗan takararta na gwamna a jihar Kano, Nasiru Koguna, bayan gaza kare kansa kan tuhuma uku
  • A wata wasika mai ɗauke da sa hannun sakataren ADP na kasa, jam'iyyar tace ta kafa kwamitoci su rarrashi waɗanda suka fusata a Kano
  • Bayan sauya shekar Sha'aban Sharaɗa, ADP ta yi ikirarin Koguna ya janye takara amma ya musanta zargin

Kano - Jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) ta kori Nasiru Hassan Koguna, tsohon ɗan takararta na gwamnan jihar Kano kan ja-in-ja da wanda ya maye gurbinsa, Shaaban Sharaɗa.

Daily Nigerian ta tattaro cewa tun da farko an zaɓi Koguna a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a babban zaɓen 2023 karkashin inuwar ADP kafin ya janye wa Sharaɗa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin Da Yasa Muka Gaza Tunɓuke Shugaban PDP Kamar Yadda Wike Ya Bukata, Atiku

Sharaɗa da Nasiru Koguna.
Kano 2023: Jam'iyyar ADP Ta Su Rarara Ta Kori Dan takarar Gwamna Kan Abu Guda Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A wata wasika mai adireshin Koguna ɗauke da sa hannun sakataren ADP na ƙasa, Victor Fingesi, jam'iyyar tace tun farko ta kafa kwamitoci biyu da nufin sasanta rikicin Kano da rarrashin mambobin da suka fusata amma Koguna yaƙi biyayya.

Bisa hujjar gaza bayyana gaban Kwamitoci ya kare kansa kan tuhume-tuhumen da ake masa da suka haɗa da, rashin ladabi, rashin kunya da cin amanar jam'iyya yasa aka ɗauki wannan matakin a kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashin wasiƙar yace:

"Biyo bayan shawarin da kawamitici biyu da aka kafa domin su magance rikicin Kano suka bayar, wanda kana ɗaya daga cin manya-manya. Idan baka manta ba kwamiti ya gayyace ka don bin ƙa'idoji amma ka ƙi zuwa."
"Bisa la'akari da tanadin kwansutushin ɗin ADP, kwamitin gudanarwa na ƙasa ya yi nazarin kan rahoton kwamitoci kuma ya cimma matsaya kamar haka: cewa ka yi rashin ɗa'a, kunya da bata sunan shugabannin jam'iyya."

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu, Wani Gwamnan APC Ya Faɗi Wanda Yake Kaunar Ya Gaji Buhari a 2023

"Saboda haka an kore ka daga kasancewa namban ADP daga yau ranar 9 ga watan Satumba, 2022. Daga yanzu kai (Hasaan Koguna) ya haramta ka ayyana kanka a matsayim mamban ADP ko wakiltar jam'iyya."

Bugu da ƙari jam'iyyar ta umarce shi da ya tattara duk wasu kayayyakin da suke mallakin ADP ya miƙa wa shugaban jam'iyya reshen Kano, Hon. Rabiu Bako, ba tare da bata lokaci ba.

PDP ta fara zarcin jiga-jigan APC a Katsina

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Fara Zawarcin Jiga-Jigan APC, Ta Dira Gidan Tsohon Sakataren Gwamnati

Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta fara zawarcin tsohon Sakataren gwamnatin Jiha, Dakta Mustapha Inuwa.

Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Sanata Lado Ɗanmarke, ya ziyarci Inuwa tare da rokon ya yafe abinda PDP ta masa a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel