Rade-radin Rigima: Bola Tinubu Ya Yi Bayani Kan Alakarsa da Shugaban APC na Kasa
Asiwaju Bola Tinubu ya taka zuwa sakatariyar jam’iyyar APC a Abuja tare da manyan ‘yan gaban goshinsa
‘Dan takaran ya karyata maganar da wasu ke yi na cewa bai shiri da shugaban jam’iyyar APC na Najeriya
Tinubu ya yabi wadanda suka zabe shi a zaben gwani, ya godewa Abdullahi Adamu na gudumuwar da ya ba shi
Abuja - Asiwaju Bola Tinubu mai harin zama shugaban Najeriya a karkashin APC yace babu rikici tsakaninsa da shugaban jam’iyyarsa, Abdullahi Adamu.
Vanguard tace Asiwaju Bola Tinubu ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba 2022, a nan ya gana da shugabanninsa.
Bola Tinubu ya musanya rade-radin da ake yi na cewa babu jituwa tsakaninsa da Sanata Abdullahi Adamu wanda yake rike da shugaban APC a matakin kasa.
“Ga masu kirkirar jita-jita, na karanta labari a wasu jaridu a game da sabanina da shugaba (na jam’iyyar APC na kasa), wannan katuwar karya ce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba su san mun yi nisa, mun wuce nan ba. (Abdullahi) Adamu mutum ne mai cike da hikima."
- Asiwaju Bola Tinubu
Tinubu: Zan zama Shugaban kasa
Tare muka yi Gwamna, yanzu Ubangiji ya sake hada mu wannan tafiya, zai taimaka mani a matsayin shugaban jam’iyya, in zama shugaban kasa.
Tinubu yake cewa yana da tabbacin Sanata Abdullahi Adamu zai jagoranci jam’iyyar APC ga nasara a zaben 2023 ta yadda zai karbi mulkin Najeriya.
Premium Times ta rahoto ‘dan takaran yana cewa ya ji dadin kawo ziyara zuwa babban ofishin APC, yake cewa da gaske za su shiga zabe mai zuwa.
“Za su iya fadan duk abin da suka ga dama, su yi duk abin da suke so, jam’iyyarmu a shirye ta ke domin ganin ta kawo gyara, Najeriya ta samu cigaba.”
“Abin farin ciki da karramawa ne mu zo nan, musamman ni a karon kai na domin haduwa da wadanda suka sa na zama ‘dan takaran jam’iyyarmu.”
“Ga duk ‘yan jam’iyya da ke halarce a ranar nan, ina so in yi maku godiya, tafiya tayi tafiya a matsayinmu na jam’iyyar siyasa, mun rike akidar cigaba.”
- Asiwaju Bola Tinubu
Tinubu ya gyara Legas?
An ji labari Tunde Bank-Anthony yace maganar cewa ‘dan takaran na jam’iyyar APC a zaben Shugaban kasa ya gina Legas, karya ne domin dama can an gyara jihar
Bank-Anthony yana zargin Magoya bayan APC da tattara ayyukan Tunde Fashola, da Akinwumi Ambode, da Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin na Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng