Wike da Jerin Sauran Masu Harin Shugaban Kasa da Suka Ki Yin Zama da Atiku
- Atiku Abubakar ya zauna da wadanda suka nemi tikitin shiga takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP
- Abin da ya bada mamaki shi ne wasu da aka yi takarar da su a zaben fitar da gwani sun ki zuwa wajen taron
- Ba ayi mamakin rashin halartar Gwamna Nyesom Wike ba, an nemi har irinsu Udom Emmanuel, ba a gani ba
Abuja - A wannan rahoto, mun kawo jerin wadanda suka ki halartar taron da aka yi da Atiku Abubakar, a cikin ‘yan PDP da suka shiga zaben fitar da gwani.
Dama can an san babu jituwa tsakanin ‘dan takarar shugaban kasar da gwamnan jihar Ribas, amma sai aka ga ba shi kadai ne bai sa kafa a wajen taron ba.
Legit.ng Hausa ba ta da labarin ko Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal da Bala Mohammed sun samu zuwa wajen wannan zaman da aka yi a Abuja.
Aminu Tambuwal ya ba Atiku gudumuwa a zaben, Bala Mohammed ya koma takarar gwamna, inda Saraki ya nuna yana goyon bayan 'dan takaran na 2023.
The Cable ta tabbatar da cewa ba a ga keyar Gwamna Wike yayin da aka hadu ba.
Wadanda ba a gani a taron ba:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Nyesom Wike
2. Ayodele Fayose
3. Udom Emmanuel
4. Anyim Pius Anyim
5. Sam Ohuabunwa
Daily Trust tace daga cikin wadanda suka je wannan taro akwai Mohammed Hayatu-Deen wanda tun kafin a fara zaben fitar da gwanin, ya janye takararsa.
Wazirin Adamawa ya sha alwashi zai aiki da duka abokan hamayyarsa na zaben tsaida gwani, ya kuma yi masu godiya a kan yadda suka rungumi kaddara.
A duk cikin wadanda suka nemi tikitin PDP a bana, Tari Oliver ce kadai mace.
Su wanene suka samu zuwa wajen taron?
1. Dele Momodu
2. Tari Oliver
3. Charles Ugwu
4. Kalu Chikwendu
5. Mohammed Hayatu-Deen
Peter Obi zai kawo cikas
Ku na da labari ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, Ifeanyi Okowa yace sun yi fatan ina ma Peter Obi bai shiga takara ba, domin zai jika masu aiki.
Ifeanyi Okowa yace a yankin Kudu maso gabashin Najeriya, zaben 2023 zai kasance tsakanin PDP da LP ne, Ifeanyi Okowa yace ba a yin batun APC ko su NNPP.
Asali: Legit.ng