Cikin Okowa Ya Duri Ruwa, Ya Fadi ‘Dan Takara 1 da Zai Kawo Masu Cikas a 2023

Cikin Okowa Ya Duri Ruwa, Ya Fadi ‘Dan Takara 1 da Zai Kawo Masu Cikas a 2023

  • Gwamna Ifeanyi Okowa ya nuna akwai yiwuwar su fuskanci kalubale daga wajen Peter Obi a zaben shugaban Najeriya
  • Ifeanyi Okowa mai neman mataimakin shugaban kasa a PDP yace ‘Dan takaran na Labour Party zai raba masu kuri’u
  • A cewar Okowa, za a gwabza tsakanin PDP da LP a Kudu maso gabas, yace ba maganar jam’iyyar 'Yan APC ake yi ba

Delta - ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Arthur Okowa, ya nuna tsoronsa a game da takarar Peter Obi a zabe mai zuwa.

Daily Independent newspaper tayi hira da Gwamnan na jihar Delta, a nan yace Peter Obi abin tsoro ne musamman a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Peter Obi ya yi gwamna a jihar Anambra, yanzu yana neman shugaban kasa a inuwar Labour Party. Shi Okowa ya fito daga bangaren kudu maso kudu.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Tona Abin da Ya Sa Buhari ya Zarce, Aka Doke Atiku a zaben 2019

A tattaunawar da aka yi da shi, Ifeanyi Okowa yace inda za a samu matsala shi ne akwai mutanen Kudu da za su zabi Obi domin ya fito daga wurinsu.

Ina ma Obi bai fito takara ba

"A kudu maso gabas, takarar za ta zama matsala domin ra’ayin mutane da ake samu; amma na san PDP tayi karfi a kudu maso gabas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Na san zabe a yankin kudu maso gabas zai kasance tsakanin PDP ne da LP. Muna fatan ina ma shi (Peter Obi) bai shiga takarar nan ba.
Ifeanyi Okowa
Atiku da Ifeanyi Okowa Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter
Amma tun da yana neman mulki, zai kasance tsakanin jam’iyyu biyu a kudu maso gabas, ba APC ba, sai dai PDP da jam’iyyar LP.

- Gwamna Ifeanyi Okowa

Jaridar Independent tayi wa Okowa tambaya a game da yadda sabani ya shiga tsakanin bangarorin jam’iyyar PDP saboda Atiku Abubakar ya dauko shi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yadda Tinubu da Gwamnonin PDP 4 Ke Shirya Yarjejeniyar Taimakon Juna

Rikicin Atiku v Wike a PDP

Gwamnan yace dauko shi da Atiku ya yi ikon Ubangiji ne domin akwai mutane da yawa da suka cancanta su samu takarar mataimakin shugaban kasa.

Amma duk da haka, ‘dan takaran ya nuna suna kokarin shawo kan Gwamna Nyesom Wike, yace dama ba zai yiwu a zauna a jam’iyya ba tare da rikici ba.

“Kamar yadda kuka sani, ‘dan takaranmu ya gana da Wike a Abuja da kuma a kasar waje tare da wasu abokan aikinmu. Nayi imani, za a magance wannan.”

- Gwamna Ifeanyi Okowa

Atiku da zaben 2023

Dazu kun fahimci cewa a tarihi, an yi lokacin da Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suka taimakawa Atiku Abubakar a zaben shugabancin kasa.

A zaben 2023 da na 2015 ne kowa ya yi ta kan shi tsakaninsa da Atiku Abubakar, amma sai da kowanensu ya taba marawa Atiku baya a tafiyar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng