2023: An Warware Rikicin Atiku da Wike, Wuka Da Nama Na Hannun NWC, Inji Kudan
- Ɗan takarar kujerar gwamnan Kaduna a inuwar PDP, Isah Ashiru Kudan, yace sun yi nasarar warware saɓanin Atiku da Wike
- A jiya ne, Ashiru da takwarorinsa masu neman kujerar gwamna a jihohi 16 suka ziyarci gwamna Wike na Ribas kan rikicin PDP
- Da yake jawabi a madadin 'yan takarar, Ashiru yace zasu nemi zama da kwamitin gudanarwa na kasa domin ɗaukar mataki
Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a inuwar jam'iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan, yace sun samu nasarar warware saɓanin dake tsakanin Atiku Abubakar, da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Ɗan takarar ya ƙara da cewa a halin yanzu sun shirya zasu gana da kwamitin gudanarwa (NWC) na jam'iyyar PDP ta ƙasa domin ɗaukar mataki na gaba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ashiru ya yi wannan jawabin ne biyo bayan ganawarsa da takwarorinsa na jihohi 16 da gwamna Wike ranar Talata da daddare a Patakwal, babban birnin jihar Ribas.
Yan takarar gwamnonin jihohin sun gana da Wike ne kwanaki kaɗan bayan sun yi taro da ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar a Abuja, Jaridar Punch ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi a madadin yan takarar gwamnan jim kaɗan bayan gana wa da Wike a sirrance, Isah Ashiru yace:
"Tattaunawar ta yi daɗi kuma an baje komai babu ɓoye-ɓoye. Mun tattauna batutuwan da suka shafi halin da jam'iyya ta tsinci kanta."
Wace nasara suka cimma a taro da Wike?
Ashiru, wanda ya ƙi bayanin abinda taron ya kunsa, ya ƙara da cewa, "Amma mun cimma ga ci. Mun tattauna da ɗan takarar shugaban ƙasa, mun zo nan wurin ɗan uwan mu kuma aboki (Wike)."
"Abubuwan da suka faru mun lalubo hanya mun warware su, batutuwan nan sun zo karshe a iya gani na domin nun saurari kowane ɓangare. Zamu gana da kwamitin gudanarwa na ƙasa domin ɗaukar mataki."
A wani labarin kuma Gwamnan APC Ya Fallasa Wanda Wike da Wasu Gwamnoni Suka Amince Ya Gaji Buhari a 2023
Gwamnan Ebonyi yace baki ɗaya takwarorinsa na yankin kudancin Najeriya bakinsu ɗaya kan wanda zai gaji Buhari a 2023.
Gwamnan ya bayyana cewa Wike da sauransu sun zauna tun a baya sun cimma matsaya kan tsarin karɓa-karba.
Asali: Legit.ng