An Shigar da Kara Domin Hana Kwankwaso da Abokin Takararsa Neman Shugaban Kasa
- Lauyan jam’iyyar Action Alliance ya nemi a hana Rabiu Musa Kwankwaso da Isaac Idahosa yin takara a zaben 2023
- Kafin a yanke hukunci sai ga wani bangaren ‘yan jam’iyyar AA sun je kotu, suna kalubalantar wadanda suka kai karar
- Oba Maduabuchi SAN yace wadanda suka shigar da karar ‘yan takaran NNPP ba su da hurumin magana a madadin AA
Abuja - An gamu da cikas a wata kara da jam’iyyar Action Alliance (AA) ta shigar a kotu, tana kalubalantar takarar Rabiu Musa Kwankwaso a 2023.
Daily Trust tace jam’iyyar adawa ta AA ta je babban kotun tarayya mai zama a Abuja, tana so a hana Rabiu Kwankwaso da Isaac Idahosa neman mulki.
Bangaren su Adekunle Rufai Omo-Aje da Suleiman Abdulmalik na jam’iyyar ne suka shigar da wannan kara, amma a ranar Talata aka kalubalance su.
Wasu ‘yan bangare dabam sun dumfari kotu a jiya, suka ce Omo-Aje da Ambasada Suleiman Abdulmalik ba su da hurumin da yin kara da sunan AA.
Kotu ta sauke ku daga kujerunku - Maduabuchi
Kamar yadda rahoton ya bayyana, mai gabatar da wannan kara ta bakin Lauyansa Oba Maduabuchi (SAN), yace jam’iyya ta bar hannun Kenneth Udeze.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lauyan ya nunawa kotun tarayyar cewa Alkalin kotun daukaka kara ya tsige ‘yan majalisar Udeze a wata shari’a mai lamba CA/ABJ/CV/189/2021 da aka yi.
A dalilin wannan, Oba Maduabuchi (SAN) ya kafa hujja da cewa Adekunle Rufai Omo-Aje ko Abdulmalik ba su isa su je kotu a madadin jam’iyyar AA ba
Babban lauyan ya yarda Omo-Aje da Abdulmalik sun rike shugabancin jam’iyyar a matakin kasa.
NNPP ta saba dokar zabe - AA
Jam’iyyar ta kai kara a kotu inda ta hada da hukumar INEC, NNPP, Rabiu Kwankwaso da Isaac Idahosa, tana zargin an saba doka wajen tsaida su takara.
Lauyan AA, Ukpai Ukairo ya nemi a hana Sanata Kwankwaso da Idahosa yin takarar shugaban kasa saboda NNPP ba ta kai sunayen ‘yan takara da wuri ba.
Mai shari’a Emeka Nwite ya saurari korafin kowane bangare, ya umarci a sake shigar da sabon kara a ranar 19 ga watan Satumba, domin ya yanke hukunci.
Ana haka ne sai Malachy Nwaekpe ya bada sanarwar ya rubuta murabus, ya bar jam’iyyar AA, kafin yanzu shi ne mai bada shawara kan harkar shari’a.
APC ta dakatar da 'Dan ta
A karshen makon da ya gabata ne labari ya zo cewa shugabannin APC a jihar Ogun sun dakatar da Dare Kadiri daga Jam’iyya saboda zargin zagon-kasa.
Ana tuhumar Hon. Dare Kadiri da haduwa da ‘dan takaran Jam’iyyar PDP da nufin karya jam’iyyarsa a 2023 domin bai goyon bayan Gwamna ya zarce.
Asali: Legit.ng