Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP Ya Yi Wata Ganawa Sirri da Tsoffin ’Yan Majalisu
- Dan takarar shugaban kasa a PDP ya gana da jiga-jigan siyasan kasar nan domin neman goyon bayansu
- Atiku Abubakar ya fadi abubuwa biyu da ya karu dasu a ganawar tasa ta tsoffin shugabanni da mambobin majalisa
- Zaben 2023 na kara matsowa, 'yan takara a jam'iyyu daban-daban na neman goyon baya daga manyan 'yan siyasan Najeriya
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya gana da wasu tosffin shugabanni da majalisun dokokin Najeriya domin neman goyon bayansu a manufarsa ta gaje Buhari a zaben 2023.
Atiku Abubakar ne mai rike da tutar jam'iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, inda zai gwabza da Tinubu a APC da sauran jiga-jigan siyasan kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda yace ya fa'idantu da ganawar, inda yace an tattauna abubuwa masu amfani da suka shafi kasa da makomar siyasa.
A rubutun da ya yada a Twitter, Atiku ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yanzu na kammala ganawa da tsoffin shuwagabanni da 'yan majalisar wakilai a ‘Yar’adua Center dake Abuja. Ganawar ta ba da fa'ida biyu; neman goyon bayansu a kokarin gina hanya daga tushe a tafiyar kamfen din zabe mai zuwa.
"Fa'ida ta biyu kuwa ita ce duba ga fahimtar 'yan majalisu game da wasu gyare-gyaren da ya kamata mu yi amfani dasu. A takaice dai, ganawa ce da ta yi amfani, kuma ina godiya da suka mutunta gayyatar da na yi musu."
'Yan takarar shugabancin Najeriya na ci gaba da tuntubar jiga-jigan siyasan kasar nan domin neman goyon baya a zabukan da ke tafe a nan kusa cikin shekara mai zuwa.
Jerin 'Yan Siyasan Najeriya da Kungiyoyin Dake Yiwa Tinubu Gangamin 2023
A wani labarin, ya zuwa yanzu dai Tinubu ya yi cudanya da jiga-jigan siyasa a ciki da wajen Najeriya yayin da yake ci gaba da tallata aniyarsa ta neman gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
A yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, tsohon gwamnan na Legas sananne ne wajen kitsawa da daura wasu fitattun 'yan siyasa a kujeru daban-daban, musamman gwamnoni.
Ba iya nan kadai ba, Tinubu na alfahari da ba wasu 'yan siyasa damar cimma burinsu na mulki a yankin nasu.
Asali: Legit.ng