APC ta Dakatar da Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Saboda Hada-kai da PDP
- A karshen makon da ya gabata ne Shugabannin APC a jihar Ogun suka dakatar da Dare Kadiri daga Jam’iyya
- Ana zargin Hon. Dare Kadiri da haduwa da ‘dan takaran Jam’iyyar PDP da nufin karya jam’iyyarsa a 2023
- ‘Dan majalisar yace maganar banza ake yi domin tun farko bai yi mubaya’a ga shugabannin mazabarsa ba
Ogun - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Ogun, Dare Kadiri ta gamu da matsala a jiya yayin da aka dakatar da shi daga jam’iyya a dalilin zargin shi da laifi.
Daily Trust tace an dakatar da Honarabul Dare Kadiri daga APC mai mulki ne saboda tuhumarsa da ake yi na yi wa jam’iyya zagon-kasa a jihar ta Ogun.
Shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Kadiri a karamar hukumar Ijebu ta Arewa suka dauki wannan mataki kan ‘dan majalisar dokokin mai-ci yanzu.
Kadiri wanda aka fi sani da Maba a garin Ijebu ya taba rike kujerar mataimakin shugaban majalisar dokoki, daga baya aka tunbuke shi daga matsayin.
Hon. Dare Kadiri ya karbi bukuncin ‘dan takarar gwamnan Ogun a PDP watau Ladi Adebutu kwanaki, ya sha alwashin zai yaki Gwamna Dapo Abiodun.
Kansilan Ijebu ya yi magana
Kamar yadda Sakatare da Kansilarsa a Ijebu suka sanar, sun ce an tabbatar da dakatarwar da aka yi wa ‘dan majalisar a taron shugabanni da aka yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Olarenwaju Abiodun da Sobonojo Adeniyi sun ce shugabannin jam’iyyar APC na zargin Kadiri da hada-kai da ‘yan adawa da nufin karya Dapo Abiodun.
An dakatar da Hon. Oluwadare Kadiri (Maba)
Jawabin Abidosun da Adeniyi yace mutum 19 a cikin 27 a majalisar shugabannin APC a matakin mazabar karamar hukumar sun amince da dakatarwar.
Premium Times ta rahoto Sakataren yada labarai na APC, Tunde Oladunjoye yana cewa mafi rinjaye duk sun zabi a dakatar da Hon. Oluwadare Kadiri.
“Eh (gaskiya ne). Matsaya ne da mu ka dauka a matakin mazaba.
- Tunde Oladunjoye
Aikin banza ne - Hon. Kadiri
Amma rahoto yace nan take aka ji Kadiri yana cewa wasu marasa aikin yi ne suka yi wannan zama, yace shi bai sa da zaman shugaban APC na mazabarsa ba.
Maba yace tun farko babu wanda ya zabi shugaban jam’iyya na mazabar, kuma ana shari’a a kotu domin raba gardama game da darewa kan kujerar da ya yi.
“Ba a yin abu haka kurum. Babu wanda ya gayyace ni, ban san laifi na ba. Ba su da hankali. Ban ga takarda ba, a shafukan sada zumunta na ke ji.”
- Hon. Oluwadare Kadiri
Siyasar Kano
Ku na da labari Sha’aban Sharada zai nemi takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar hamayya ta ADP, bayan ya fice daga APC mai mulki.
Jam’iyyar ADP ta fara karfi a Kano, Aminu Ladan watau Alan Waka da Adam Abdullahi Adam (Abale), suna cikin ‘yan takaranta a zaben 2023.
Asali: Legit.ng