Yahaya Bello Ya Kallafa Miliyoyi kan Tinubu, Atiku da Sauran 'Yan Siyasa Kafin Ya Bari su yi Kamfen a Jiharsa
- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya kallafa N10 miliyan ga Tinubu, Atiku, Obi da duk wani 'dan takarar shugaban kasa da zai manna fosta ko kafa allon bango don kamfen
- Ba su kadai ya saka wa wannan harajin ba, 'yan takarar gwamna a jihar zasu biya N5m, masu takarar kujerun sanatoci N2m, majalisar wakilai N1m, 'yan majalisar jiha N500,000
- Kamar yadda majalisar jihar ta bayyana , za a kafa hukuma da zata kula tare da bada dama ga wadanda suka biya tare da kiyaye inda zasu mannan fostoci a jihar yayin kamfen
Kogi - Sabuwar dokar jihar Kogi ta kallafa miliyan goma kan 'yan takarar shugabancin kasa a zaben 2023 kafin a bar su saka fastoci da manyan allunan kan titi na kamfen.
Wasu daga cikin 'yan takarar shugabancin kasan da hakan ya shafa sun hada da Sanata Bola Tinubu na jam;iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Peter Obi na jam'iyyar LP da Peter Umeadi na jam'iyyar APGA da sauransu.
Hakazalika. 'yan takarar kujerar gwamna a jihar zasu biya N5 miliyan yayin da masu takara kujerun sanatoci zasu biya N2 miliyan da 'yan majalisar wakilai zasu biya N1 miliyan.
Wadanda ke son takarar kujerar majalisar jihar da ciyamomi zasu biya N500,000 kafin a bar su suyi kamfen dinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan biyan kudin na dole ya biyo bayan sabuwar dokar da majalisar jihar Kogi ta kafa kafin zuwan zaben, Arise TV ta rahoto.
Majalisar jihar karkashin shugabancin Honarabul Mathew Kolawole, bayan amincewa da rahoton kwamitin hadin guiwar majalisar a kan kasuwaci da shari'a, yace dokar zata daidaita tallace-tallace a jihar.
'Yan majalisar sun kara da cewa, hakan zai shawo kan matsalar manna fostoci a kan hanyar wucewa, bango, gadoji da sauran wurare dake bata jihar.
Dokar ta bukaci kafa hukuma wacce zata daidaita wadannan lamurran kuma za a bada shaida ga duk wani mutu ko kungiya da zata manna fostoci ko ta kafa allunan kan titi a inda ya dace.
Yadda Tinubu da Tawagar Wike Ke Shirya Yarjejeniyar Nasara a Zaben 2023
A wani labari na daban, akasin yadda ake ta hasashe kan cewa tsagin Gwamna Wike na jam'iyyar PDP zasu koma APC bayan ganawarsu da 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, an gano cewa aiki suke tare don ganin nasarar APC a zaben shugaban kasa, Vanguard ta tabbatar da hakan.
Dukkan bangarorin biyu sun gana a UK wanda ya janyo aka dinga hasashen cewa gwamnonin PDP da suka hada da Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu tare da Nyesom Wike suna shirin sauya sheka ne.
Bayan dawowar Wike daga Landan da kuma ganawarsa da Tinubu, yace sun tattauna ne kan abubuwan da suka shafi Najeriya. Sabon taron da za a yi tsakanin tawagar Wike da Tinubu a makon nan mai zuwa kamar yadda majiyoyi suka ce, za a gina ne kan yarjejeniyar aikin da suka fara a makonni biyu da suka gabata.
Asali: Legit.ng