Yadda Tinubu da Tawagar Wike Ke Shirya Yarjejeniyar Nasara a Zaben 2023
- Ba kamar hasashen da aka dinga ba, Wike tare da tawagarsa da suka zanta da Tinubu a Landan sunan nan daram a PDP babu batun sauya sheka
- Sai dai bayanai gamsassu sun bayyana cewa, gwamonin PDP hudun zasu yi wa Tinubu aiki a jiharsu domin ya lashe zaben shugabancin kasa
- A matsayin hanyar ramawa kura aniyarta, gwamnonin sun bukaci Tinubu da kada ya shiga hurumin zabukan jihohin na gwamnoni da majalisu
Akasin yadda ake ta hasashe kan cewa tsagin Gwamna Wike na jam'iyyar PDP zasu koma APC bayan ganawarsu da 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, an gano cewa aiki suke tare don ganin nasarar APC a zaben shugaban kasa, Vanguard ta tabbatar da hakan.
Dukkan bangarorin biyu sun gana a UK wanda ya janyo aka dinga hasashen cewa gwamnonin PDP da suka hada da Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu tare da Nyesom Wike suna shirin sauya sheka ne.
Bayan dawowar Wike daga Landan da kuma ganawarsa da Tinubu, yace sun tattauna ne kan abubuwan da suka shafi Najeriya.
Sabon taron da za a yi tsakanin tawagar Wike da Tinubu a makon nan mai zuwa kamar yadda majiyoyi suka ce, za a gina ne kan yarjejeniyar aikin da suka fara a makonni biyu da suka gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Koma dai mene ne, ana cigaba da tattaunawa. Duk abinda muke magana a kai, ya shafi Najeriya ne da 'yan Najeriya. Ba ya shafi mutum daya bane ko kungiya daya. Mun yarda da cewa duk abinda muke tattaunawa zai amfani 'yan Najeriya daga bisani.
"Muna cigaba da tattaunawa. Kada ku damu da wadanda basu yarda da wanzuwar kasar nan ba. Shugabanci ba don kai ko iyalanka bane. Shugabancin don kowa ne," Wike yace bayan ganawar da suka yi.
Sai dai rahotannin da suka bayyana sune, bangarorin Wike da Tinubu sun kasa daidaitawa a yayin ganawar.
Bukatunsu
An gano cewa Tinubu ya zame daga bukatun Wike na aiki tare domin samun nasara a zabe mai zuwa.
Kamar yadda majiyoyi suka ce, Wike ya bukaci 'dan takarar APC da idan ya ci zaben, wanda zabensu za a fara yi, ya tabbatar bai shiga hurumin zabukan gwamnonin da 'yan majalisar jihohin Rivers, Benue, Oyo da Abia ba ta yadda 'yan tsaginsu zasu cigaba da juya jihohin.
Ya kara da bukatar tabbacin cewa, a bar mutanensa su samu kujerun majalisar dattawa da wakilai har da gwamnoni dake neman kujerun sanatoci.
Duk da babu bangaren da suka fito suka musanta wannan lamarin, bayanai sabbi da Vanguard ta samu sun bayyana cewa dukkan bangarorin sun amince da yin aiki tare a zabe mai zuwa.
Majiyoyi da dama da suka san abinda aka zanta a London sun tabbatar da cewa babu batun sauya shekar Wike da mukarrabansa.
Sun kara da amincewa kan Wike da tawagarsa zasu zauna a PDP inda zasu dinga yi wa Tinubu aiki domin yayi nasarar lashe zaben shugaban kasa a jihohinsu.
Asali: Legit.ng