Shugabannin PDP 3 da Aka Yi da Gwamna Wike Ya yi Rigima Da Su a Jere
- Kusan duka shugabannin PDP na kasa da aka yi bayan zaben 2015 sai da suka yi fada da Gwamna Nyesom Wike
- A cikin shekaru shida, jam’iyyar adawa ta PDP ta fada hannun Ali Modu Sheriff, Uche Secondus da Iyorchia Ayu
- Da farko Gwamnan Ribas ya marawa shugabannin jam’iyyar baya, amma da tafiya tayi tafiya, ya dage a tunbuke su
Daga 2016 zuwa yau, za a ji Ahmad Makarfi ne kurum bai yi fada da Nyesom Wike ba
1. Ali Modu Sheriff
Sanata Ali Modu Sheriff ya rike shugabancin jam’iyyar PDP a 2016, amma su Gwamna Nyesom Wike suka san yadda suka yi, sai da kotu ta sauke shi daga baya.
A wani jawabi da ya fitar a lokacin ta bakin Mai taimaka masa, Simeon Nwakaudu, Gwamnan na Ribas ya zargi Ali Modu Sheriff da yunkurin wargaza jam’iyya.
Kamar yadda Wike ya fada, tsohon gwamnan na Borno ya fi dacewa ya rike PDP a lokacin da ya zama shugaban riko, amma daga baya aka ga bukatar sauke shi.
2. Uche Secondus
A karshen 2021, Nyesom Wike ya fito yayi wa Duniya bayanin abin da ya sa su ka dage sai an yi waje da Uche Secondus wanda ya zama shugaban PDP a 2017.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan yace duk da Uche Secondus ya fito daga jihar Ribas, akwai bukatar a sauke shi idan har ana son jam’iyyar PDP ta lashe zaben shugabancin kasa a 2023.
Rigimar Wike da Secondus ta kai sun samu sabani a fili a wajen wani taron BOT da aka yi. Duk da an so Secondus ya karasa wa’adinsa, sai da aka dakatar da shi.
3. Iyorchia Ayu
Bayan Mai girma Nyesom Wike sun yi nasarar dakatar a Prince Uche Secondus da ‘yan majalisarsa, sai Dr. Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban PDP a Najeriya.
Ana gama zaben fitar da gwanin shugaban kasa aka fahimci an samu rashin jituwa tsakanin bangaren Gwamna Wike da Iyorchia Ayu, aka huro masa wuta ya sauka.
Masu adawa da Ayu suna zargin ya kamata shugaban jam’iyya ya fito daga Kudu tun da Atiku Abubakar aka ba takaran 2023, Dr. Ayu dai yace ba zai yi murabus ba.
Leye Odunjo zai koma APC?
Dazu kun ji labari an samu sauyin shekar da za ta iya girgiza ‘Ya ‘yan PDP a kudu maso yammacin Najeriya, inda Leye Odunjo ya rabu da jam’iyyar adawar.
Odunjo ya rubutawa Iyorchia Ayu da Sikirulai Ogundele wasika, yace ya bar jam’iyyar, kuma ya ajiye mukamin da yake kai na mataimakin shugaban PDP a Ogun.
Asali: Legit.ng