2023: An Sake Zargin Peter Obi Da Wani Babban Abu Da Zai Iya Janyo Masa Matsala A Takarar Shugaban Kasa

2023: An Sake Zargin Peter Obi Da Wani Babban Abu Da Zai Iya Janyo Masa Matsala A Takarar Shugaban Kasa

  • An zargi tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da nuna banbanci wurin rabon mukami masu gwabi a lokacin yana gwamna
  • Wata mata mai suna Ada Anambra a Twitter ta yi ikirarin cewa kawai mabiya darikar Katolika ne kadai ake bawa manyan mukamai a gidan gwamnati
  • Joe Igbokwe, mamba na cocin Anglican ya tabbatar da zargin, yana mai cewa ba abin da ya kamata a amince da shi bane

An yi wani ikirari mai tada hankali na cewa addini ne ake amfani da shi a jihar Anambra wurin bada manyan mukamai a gwamnati.

Joe Igbokwe ne ya yi ikirarin a dandalin sada zumunta a lokacin da ya ke martani kan wani zargi irinsa da wata mai suna Ada Anambra ta yi a Twitter.

Peter Obi
Shugabancin Kasa Na 2023: An Sake Zargin Peter Obi Da Aikata Babban 'Laifi'.
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Ya Fara Tsorata, Ya Gagara Hakura da Maganar Peter Obi

A cewar matar, mabiya darikar katolika ne kawai suke samun manyan mukamai a gwamnati.

Ta yi ikirarin cewa ana karin girma da samun cigaba ne a gwamnatin jihar bisa la'akari da cocin da mutum ke zuwa, ta kara da cewa dole sai mutum ya kasance 'Roman Catholic' kafin ya samu babban makami.

Abin da ya fi tada hankali kuma shine wacce ta yi ikirarin ta ce gwamnatin Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra ce ta fara wannan abin.

Da ya ke martani kan wannan, Igbokwe ya ce shi mamba ne na cocin Anglican, kuma tabbas ya san da lamarin.

Ya bayyana al'adar a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.

Kalamansa:

"Na sha bayyana wa mutane wannan abin. Wani Bishop din Anglican cikin hawaye ya fada min abin abubuwan da ya rika faruwa da shi a hannun gwamnonin Katolika a Jihar Anambra tun 2023.

Kara karanta wannan

Rashin Sallah: Kishin Addini Ya Sa Ya Hakura da Aikin da Yake yi a Kamfanin Mai

"Ni Anglican ne daga Nnewi a Jihar Anambra kuma na san labarin nan sosai. Abin takaici ne kuma bai kamata a amince da shi ba. Ya zama dole a kawo karshen karfa-karfa da yan katolika ke yi a gidan gwamnati a Akwa."

Amma, ya zama dole a sani cewa wannan zargi ne kuma Obi bai riga ya yi martani ko karyata zargin da aka masa ba.

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na LP, Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164