Duk Bayaraben Da Yaki Zaben Tinubu Ba Dan Halas Bane, Jigogin APC

Duk Bayaraben Da Yaki Zaben Tinubu Ba Dan Halas Bane, Jigogin APC

  • Kungiyar Next Level Consolidation Forum ta yi hasashen cewa Tinubu zai samu kashi 80% na kuri'un yankin Yarbawa
  • Jigogin na APC a yankin Arewa maso yamma sun ce yanzu karon Yarbawa ne su fitar da shugaban kasa
  • A cewa kungiyar ta APC, babu Bayaraben kirkin da zai ki zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ibadan - Mambobin kungiyar Next Level Consolidation Forum, wata kungiyar masoya Tinubu, sun bayyana cewa dan takaran kujeran shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, zai samu kashi 80% na kuri'un yankin Arewa maso yamma a zaben 2023.

Shugaban kungiyar, Oladosu Oladipo, ya bayyana hakan ne a wani zama da suka yi a Ibadan, jihar Oyo.

Tinubu
Duk Bayaraben Da Yaki Zaben Tinubu Ba Dan Halas Bane, Jigogin APC Hoto: Tinubu
Asali: UGC

Sun bayyana cewa yankin Yarbawa zasu yi duk mai yiwuwa don godewa Tinubu bisa ayyukan kwarai da yayi a matsayin gwamnan Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun kara da cewa Tinubu yana da hangen nesa, ilimi, iko da karfin kawo sauyi Najeriya.

A jawabinsa, Oladosu yace al'ummar yankin kudu maso yamma sun fahimci cewa yanzu karon Yarbawa su fitar da shgaban kasa, kuma babu bayaraben da ba zai zabi nasa ba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa Oladosu ya umurci dukkan masu kamfen Tinubu su shiga kowani gunduma, lungu da sako a fadin kasar nan.

'Yan a Mutun Tinubu Sun Dura Wani Asibiti a Abuja, Sun Tallafawa Marasa Lafiya

A wani labarin kuwa, 'Yan a mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, sun yi abin kirki ta hanyar biyawa majinyata 4o kudin magani a a babban asibitin Kubwa dake babban birnin tarayya, Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa masoyan na Tinubu sun yi wannan aikin ne a gaban Daraktan Likitoci, Dokta Lasisi Muyideen da wasu manyan ma’aikatan asibitin.

Da yake zantawa da manema labarai, Shola Olofin wanda ya shirya shirin tallafin kuma shugaban tawagar gangami ta Bola Ahmed Tinubu Vanguard ya bayyana kadan daga manufar wanna ba da tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel