2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa

2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa

  • Dakta Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ya ce zai kame kansa ba zai goyi bayan kowa ba a zaben shekarar 2023
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wurin bikin cikar Bishop Matthew Kukah shekaru 70 da aka yi a birnin tarayya Abuja
  • A baya-bayan nan Mista Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja don neman ya sa masa albarka a cewar wasu majiyoyi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya ce ba zai goyi bayan kowa ba a babban zaben shekarar 2023, Premium Times ta rahoto.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 31 ga watan Agusta a wurin bikin cikar Bishop Matthew Kukah shekara 70 da aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC

Goodluck Jonathan.
2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Jonathan ya yi wannan maganan ne kwanaki kadan bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ziyarce shi a gidansa a birnin tarayya Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Tinubu shima ya halarci taron bikin tare da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima.

Jonathan ya ce:

"Kuma, za mu samu daman zaben shugabannin mu, zabe suna tafe - yanzu da muke maganan zabe, na lura cewa ban gane Asiwaju Bola Tinubu ba, dan takarar shugaban kasa na APC da abokina, Kashim Shettima.
"Zaben dama ce mai kyau ga yan Najeriya su zabi wanda suke ganin zai iya jagorantar kasar. Na yanke shawarar ba zan goyi bayan kowa ba a matsayin tsohon shugaban kasa. Zan kame kai na."

Bola Tinubu Ya Nemi Alfarma Daya a Wurin Jonathan Kan Zaben 2023

A wani rahoton, mai neman kujerar shugaban kasa karkashin inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonthan a Abuja a wani ɓangare na ci gaba da ziyarar neman goyon baya gabanin 2023.

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Duk da ba'a bayyana abinda suka tattauna ba, amma wata majiya daga cikin tawagar Tinubu ta shaida wa wakilin Punch cewa ziyarar wani ɓangare ne na ƙara faɗin neman shawari daga masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.

Majiyar ta bayyana cewa yayin ziyarar Bola Tinubu ya nemi alfarmar goyon baya daga wurin tsohon shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164