Yunkurin Tsige Buhari: Sirikinsa Ya Magantu Kan 'Yan Malisar Tarayya

Yunkurin Tsige Buhari: Sirikinsa Ya Magantu Kan 'Yan Malisar Tarayya

  • Sirikin shugaban Buhari, Alhami Mohammad Sani Sha'aban, yace barazanar tsige Buhari daga kujerarsa wasa ne da abun dariya
  • Ya caccaki 'yan majalisar dokokin Najeriya kan cewa suna da hannu a kalubalen tattalin arziki da tsaro da ya addabi kasar nan
  • Ya bayyana cewa, kawai so suke su doka mugun misali da Buhari saboda sun rasa abinda zasu sanar da mutanen mazabunsu kan gazawarsu

Tsohon 'dan majalisar wakilai kuma 'dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna na 2023 a zaben fidda gwanin APC, Alhaji Sani Sha'aban yace barazanar da majalisar tarayya ke yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari wasa ne.

Sha'aban wanda sirikin Buhari ne, yace 'yan majalisar da kansu suna da alhakin kalubalen tattalin arziki da tsaron da ya addabi kasar nan, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari ga Gwamnonin APC: Ba Zan Tsoma Baki a Zaben 2023 ba

Sani Sha'aban
Yunkurin Tsige Buhari: Sirikinsa Ya Magantu Kan 'Yan Malisar Tarayya. Hoto daga 21st Centurychronicles.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, 'yan majalisar sun gaza a ayyukansu ballantana a bangaren tsaro da tattalin arziki inda yace suna aikinsu ne kawai idan sun rasa kudi ta yadda zasu samu alawus hade da manyan jakkuna.

Sha'aban wanda ya zanta da manema labarai a Kaduna ranar Laraba, ya kwatanta barazanar tsige Buhari da abun dariya kuma wasan ba'a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa mambobin majalisar tarayyan suna wannan barazanar ne saboda zabe inda yace 'yan majalisar da suka gaza a aikin wakilcinsu kuma sun rasa abinda zasu fadawa mazabunsu suke neman a sake zabensu, suke yunkurin tsigewar saboda suna son amfani da shugaba Buhari matsayin misali maras kyau.

Sha'aban wanda ya taba wakiltar mazabar Zaria a majalisar tarayya tsakanin 2003 zuwa 2007 yace:

"Ina kallon matsayar majalisar dattawan a matsayin babban wasa. A takaice dai, abun dariya ne.

Kara karanta wannan

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

"Abinda ya dace mu sani shi ne Najeriya bata aiki ita kadai, sauran duniya suna kallonmu. A damokaradiyya muke duk da mun aro tsarin ne daga turawa da sauran sassan duniya kamar yadda suke nasu.
"Mu sani cewa a majalisar wakilai, dattawa, suna aiki ne karkashin kwamiti daban-daban kuma kwamitocin suna kula da wasu ayyukan na musamman ne. Amma me ke faruwa a yau? Wanne aikin suke yi? Me ke faruwa ga rahotannin ayyukan tsaron da ake yi?
"In har wani zai tashi a yau, ya zo majalisa tare da zargin Buhari kan tsaro, ina kalubalen ta tsada ya je ya tsige shi gobe idan zai iya.
"A yayin da kake dora laifi kansa, miliyoyin mutane daga mazabarka suna dora laifi a kan ka. Kun ce kuna wakiltarsu, shine kuke son amfani da Buhari matsayin misali maras kyau?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel