Da Duminsa: Shekarau Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Bayan Wata 3 Rak a NNPP

Da Duminsa: Shekarau Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Bayan Wata 3 Rak a NNPP

  • Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya bar jam'iyyar NNPP
  • Hakan yana zuwa ne bayan wata uku rak da barin jam'iyyar APC inda yanzu ya koma jam'iyyar PDP kacokan
  • Ya samu tarba hannu bibbiyu daga Atiku Abubakar, Ifeanyi Okowa, Namadi Sambo, Sule Lamido, Attahiru Bafarawa da sauransu

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya sanar da barin jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari zuwa ta PDP.

Wannan na zuwa ne kasa da watanni uku bayan shekarau ya bar jam'iyyar APC inda ya koma ta NNPP.

Atiku da Shekarau
Da Duminsa: Shekarau Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Bayan Wata 3 Rak a NNPP. Hoto daga @thecable
Asali: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa, Shekarau ya bayyana barin NNPP a ranar Litini a gidansa dake Mundubawa dake jihar Kano.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Mashahurin Mai Kudin Duniya, Elon Musk, Yace Mahaifiyarsa a Gareji Take Kwana Idan ta Kai Masa Ziyara

Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka hada da Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa na PDP, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu da sauransu.

Shekarau ya kara da cewa, ya aike da wasika ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, domin sanar da janyewarsa daga takarar kujerar sanatan Kano ta tsakiya karkashin jam'iyyar NNPP.

Sauran manyan da suka halarci wurin sanar da sauya shekar sun hada da: 'dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa; gwamnonin Sokoto da Taraba, Aminu Waziri Tambuwal da Darius Ishaku.

Akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar, tsofaffin gwamnonin Sule Lamido, Attahiru Bafarawa, Ahmed Makarfi, Boni Haruna da sauransu.

Bangaren Shekarau Ta Magantu Kan Jita-Jitar Komawarsa PDP

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi watsi da tayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar na komawa PDP.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

Hadimin Sanata Shekarau, Malam Bello Sharada, ya fada wa Sahelian Times a ranar Talata, ya kara da cewa kwamitin Shura ta Ibrahim Shekarau ta yi amincewa da neman da PDP ke yi na sanatan da ke wakiltan Kano Central ya koma PDP.

Sharada ya kara da cewa a yayin taron da aka yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta na 2022 a gidan Shekarau na Mundubawa a Kano, an tattauna wasu muhimman abubuwa baya da tayin da Atiku Abubakar ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel