Shugaban NNPP Ya Fadi Babban Abin da Ya Wargaza Taron Dangin Kwankwaso/Obi

Shugaban NNPP Ya Fadi Babban Abin da Ya Wargaza Taron Dangin Kwankwaso/Obi

  • Kwanakin baya an yi yunkurin yin taron dangi tsakanin bangaren jam’iyyar NNPP da tsagin jam’iyyar LP na Peter Obi
  • Wannan magana ba ta kai ko ina ba ta rushe, bayan kowace jam’iyya tace ita za a sallamawa takarar shugaban kasa a 2023
  • Shugaban NNPP a Najeriya, Farfesa Rufai Alkali ya yi bayani kan abubuwan da suka jawo aka samu matsala a tattaunawar

Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufai Alkali ya yi karin haske a kan yadda taron dangin NNPP da LP ta ruguje kwanakin baya.

Daily Trust ta rahoto Farfesa Rufai Alkali yana cewa an samu matsala ne yayin da ‘yan jam’iyyar LP suka ce su za a ba takarar shugaban kasa a 2023.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Abuja, Farfesan yace ‘yan bangaren Peter Obi da kuma LP ba su ba jam’iyyar NNPP wani zabi a tattaunawar ba.

Kara karanta wannan

An Raba Kan Shugabannin PDP da Batun Tunbuke Shugaban Jam’iyya daf da 2023

Shugaban jam’iyyar ta NNPP yace da farko sun sa ran cewa haduwarsu da LP za ta yiwu a 2023. A karshe dai kowa zai yi takara a inuwar jam'iyyarsa.

Kamar yadda ya shaidawa manema labarai a ranar Lahadi, da aka fara zama, babu abin da jam’iyyar LP take cewa illa a damka mata tikitin takara.

NNPP.
Magoya bayan Kwankwaso a Borno Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Inda aka samu matsala

“An kafa kwamiti da zai duba yiwuwar haduwar, amma a tsawon awanni takwas da aka zauna, bangaren LP sun yi ta fadan abu daya ne;
Kwankwaso ya hakura da takarar shugaban kasa, ya sallamawa Obi, su na cewa lokacin ‘Yan Kudu maso gabas ne suka karbi shugabanci."

- Farfesa Rufai Alkali

Duk da sabanin da aka samu, Farfesa Alkali ya bayyana cewa ‘yan jam’iyyar hamayyar ta LP sun gamsu Kwankwaso ‘dan takara ne mai abin tallatawa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

Fallasa sirrin tattaunawa

Ana haka kuma sai ‘yan bangaren Peter Obi suka rika fito da sirrin tattaunawar da ake yi, su na yadawa a shafukan sada zumunta da dandalin yada labarai.

Rahoton yace wannan fallasa sirrin shirin da ake yi, ya taimaka wajen ruguza hadin-gwiwar.

Alkali ya kuma ce ba a kai ga karasa magana ba, an yi carko-carko sai wakilan LP suka shaidawa Duniya cewa yunkurin yin taron dangi da NNPP ya lalace.

Rigimar nada sabon shugaba a PDP

Kun ji labari cewa daga cikin manyan bukatun Nyesom Wike da mutanensa shi ne a san yadda za ayi a tunbuke Iyorchia Ayu daga shugabancin PDP na kasa.

Amma kuma a tsarin mulki, ko da an sauke Dr. Iyorchia Ayu, abin da su Wike ba su so, mataimakin shugaban PDP na Arewa ne zai zama shugaban jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng