Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja
- Tsohon gwamnan Legas kuma ɗan takarar shugaban kasa na APC ya gana da shugaban APC da jiga-jigai a Abuja
- Bola Tinubu da Shettima sun gana da jagororin APC ne biyo bayan taron da ya gudana a Landan tare da gwamna Wike na PDP
- Ibrahim Masari, na hannun dama Tinubu ya yi ikirarin cewa shawo kan Wike kuma zai musu aiki a 2023
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sanata Kasshim Shettima, sun yi wata ganawa ta dabaru da wasu jiga-jigan jam'iyya a Abuja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, na daga cikin mahalarta taron tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa.
Taron wanda ya guda a Ofishin Kamfe kuma a sirrin ce, ya samu halartar mataimakin shugaban APC na shiyyar kudu maso yamma, Isaac Kekemeke, da shugaban matasa na ƙasa, Dayo Israel.
Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar arewa, Sanata Abubakar Kyari da wasu manyan jiga-jigai a kwmaitin gudanarwa NWC na ƙasa.
Hotunan wurin taro
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Me suka tattauna a wurin taron?
Punch ta tattaro cewa duk da ba'a bayyana maƙasudin taron ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoton amma wata majiya ta ce mai yuwuwa taron na da alaƙa da zawarcin gwamna Nyesom Wike da rarrashin mambobin da suka fusata.
Tinubu, wanda ke cigaba dabkokarin shawo kan gwamna Wike game da kudirinsa na maye gurbin shugaba Buhari a 2023, ya gana da gwamnan a Landan ranar Litinin.
Kwanaki biyu bayan haka, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya garzaya ya zauna da Wike a wani yunkuri da ake kallon zai murkushe duk wasu kalaman da Tinubu ya fara jawo hankalinshi da su.
A wani labarin kuma Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Darakta Janar na kungiyar masoyan gwamna Nyesom Wike ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Hakan ta faru ne yayin da wasu bayanai suka nuna Wike da wasu gwamnonin PDP sun sa labule da Bola Tinubu a Landan.
Asali: Legit.ng