Yan Sanda Sun Rufe Sabuwar Ofishin NNPP A Borno, An Kuma Kama Shugaban Jam'iyyar
- Honarabul Mohammed Attom, jagoran jam'iyyar NNPP a Borno ya yi ikirarin cewa yan sanda sun rufe sabuwar sakateriyar jam'iyyarsu kuma an kama shi
- Attom ya yi ikirarin cewa yana kyautata zaton jam'iyyar APC mai mulki a jihar karkashin Gwamna Babagana Zulum tana da hannu kan abin da ya faru da jam'iyyarsu
- A bangarensa, shugaban APC na Borno, Ali Bukar Dalori ya musanta cewa jam'iyyarsu na da hannu kan lamarin, ya shawarci NNPP ta warware matsalarta da yan sandan
Borno - Jami'an tsaro dauke da bindigu da aka zargin yan sanda ne, a safiyar ranar Alhamis sun mamaye sakatariyar jam'iyyar NNPP da ke Maiduguri, Jihar Borno kwanaki kadan kafin kaddamar da ofishin da ke kusa da Abbaganaram.
Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne a ranar Laraba bayan da shugabannin jam'iyyar suka dauki hayar leburori su musu fentin sabuwar sakatariyar, gabanin zuwan dan takarar shugaban kasarsu, Rabiu Kwankwaso don kaddamar da ofishin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma, wasu da ake zargin yan daba ne daga jam'iyyun hamayya suka kutsa sakateriyar suka lika fastocin yan takarar su a wurare daban-daban a harabar sakateriyar, Vanguard ta rahoto.
Hakan bai yi wa magoya bayan jam'iyyar ta NNPP dadi ba kuma daga bisani fada ta kaure tsakaninsu.
Wata majiya ta ce ofishin na NNPP yana unguwa ce ta gidajen mutane, hakan yasa jami'an hukumar tsara birane ta rufe shi bayan an musu gargadin su dena ginin.
Jagoran NNPP ya tabbatar da lamarin
Honarabul Mohammed Attom, dan takarar sanata na Borno Central na NNPP ya tabbatar da rufe ofishin a hirar tarho, yana cewa:
"Yan sanda da bindigu sun mamaye sakateriyar da dan takarar shugaban kasar mu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar ba tare da wani dalili ba."
Ya kara da cewa baya ga rufe sabuwar sakateriyar, yan sandan sun kama shi sun tafi da shi ofishinsu da ke Maiduguri a safiyar yau Alhamis.
Attom ya cigaba da cewa:
"Eh, zan iya tabbatar maka, yan sanda sun kama ni safiyar yau Alhamis. Yanzu haka ina ofishin yan sanda na Jihar Borno, kuma an fada min dan bada dadewa ba za a kwace waya ta.
"Na yi amfani da wannan damar in sanar da kai abin da ke faruwa ne yanzu, kuma don Allah ka fada wa duniya abin da ke faruwa da sakateriyar NNPP da ni.
"Ina zargin akwai hannun jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Babagana Zulum."
Martanin shugaban APC na Borno
A bangarensa, shugaban jam'iyyar APC na Jihar Borno, Ali Bukar Dalori ya musanta cewa APC na da hannu a lamarin kamar yadda Attom ya yi ikirari.
Ya ce:
"Ina son tabbatar maka, APC ta Jihar Borno bata da hannu cikin rufe sakateriyar NNPP kamar yadda Honarabul Attom ya yi ikirari.
"Yanzu na ke jin labarin daga wurinka, kuma idan Honarabul Attom yana hannun yan sanda, suyi kokari su sulhunta kansu, amma kada ya saka jam'iyyar mu ciki."
Martanin yan sanda
Kakakin yan sandan Borno, DSP Sani Shatambaya ya ce ba da labarin faruwar lamarin, amma kwamishinan yan sanda, CP Abdul Umar bai amsa sakon da aka tura masa ba har zuwa lokacin wallafa wannan labarin.
Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP
A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.
Asali: Legit.ng